Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano, Dan majalisa

Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano, Dan majalisa

  • Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rogo da Karaye, Haruna Isah Dederi, ya koka kan shigar yan bindiga jihar Kano
  • A cewarsa yan bindigan dake gudowa daga luguden wutan rundunar sojoji a Zamfara da Katsina sun fara kai hari ƙaramar hukumar Rogo
  • Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakile yawon yan bindiga daga wani wuri zuwa wani

Abuja - Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo/Karaye ta jihar Kano, Haruna Isah Dederi, yace saboda luguden wutan sojoji kan yan bindiga a Zamfara da Katsina, sun fara tserowa suna shiga jihar Kano.

A wani kudiri da ya gabatar a zaman majalisa na ranar Talata, yace a yan makonnin da suka gabata mahara sun kai hari wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Rogo.

Dailytrust ta rahoto cewa ƙauyukan da hare-haren ya shafa sun haɗa da Jajaye, Zarewa, Ruwan Bago, Bari, Falgore, DutsenBan da Hawan -Gwamna (Fulatan).

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

Yan bindiga sun fara kai hari Kano
Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano, Dan majalisa Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Ya kamata a ɗauki matakin gaggawa - Dederi

A jawabinsa, ɗan majalisar yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan ba'a ɗauki matakin gaggawa ba domin dakile ayyukan waɗannan yan bindigan a ƙaramar hukumar Rogo da sauran yakunan dake karshen iyakar Kano."
"Maharan zasu watsu zuwa sauran yankuna, kuma haka barazana ne ga zaman lafiyan jihar."

Wane mataki majalisa ta ɗauka?

Bayan sauraron wannan kudiri ne, majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ankare da abinda nasarar da sojoji ke samu a Zamfara da Katsina ke jawo wa.

Ta hanyar ɗaukar matakai a sauran jihohin da lamarin ya shafa domin dakatar da sauya gurin yan bindiga daga wannan wurin zuwa wani na daban.

A wani labarin kuma gwamna Masari na jihar Katsina yace gwamnonin jihohi 7 sun haɗa kai zasu ɗauki yan bijilanti 3,000

Kara karanta wannan

Ku Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta'addanci Idan Ba Tsoro Ba, PDP Ta Caccaki Gwamnatin Buhari

Masari yace akwai ƙungiyoyin yan bindiga sama da 150 a cikin dazuka, waɗanda suke da shugabanni, kuma suna da alaƙa da juna.

Yace mayunwatan yan bindiga sun fara yawo ƙauyuka domin neman kayan abinci kasancewar lokacin kawo amfanin gona gida ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel