Mutuwar Deby katuwar matsala ce gare mu - Ministan tsaro ya fadi matakan da ake dauka
- Ministan tsaro ya ce mutuwar Idris Deby matsala ce ga masu makwabta da Chadi
- Bashir Magashi ya ce babu kasar da za ta koka da rashin Idris Deby irin Najeriya
- Janar Magashi ya tabbatar cewa gwamnati za ta tabbatar da zaman lafiya a Chadi
A ranar Alhamis, Ministan harkar tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya yi magana game da kashe shugaban Chadi, Idriss Deby, da aka yi.
Janar Bashir Magashi ya bayyana cewa kisan Idriss Deby zai iya jawo wa Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da Chadi, matsalolin tsaro.
A dalilin haka gwamnatin tarayya ta ce ta inganta tsaro domin a tabbatar da wanzurwar zaman lafiya, kuma ta na bibiyar kasar da ta ke kan iyakarta.
KU KARANTA: Shugabannin Afrika da su ka bar wa ‘ya ‘yansu kujerar mulki
Jaridar Punch ta ce Janar Bashir Magashi ya yi magana ne a fadar Aso Villa a wajen taron mako-mako da ma’aikatan fadar shugaban kasa su ke shirya wa.
Ministan ya ke cewa: “Da mu ka ji labarin takaicin kashe shugaban kasar Chadi, mun san cewa matsala za ta iya auku wa a kasashen da ke makwabtaka da ita.”
“Najeriya ce za ta fi gamu wa matsala sosai a dalilin rashinsa (Idriss Deby)” inji Janar Magashi.
“Idan akwai matsalar tsaro a Chadi, za a samu matsaloli sosai. Amma mun gode wa Ubangiji, sojojinmu da yawa su na sintiri a Chadi, Nijar da Kamaru.”
KU KARANTA: Idriss Déby Itno ya taba yi wa Boko Haram lahanin da ya fusata Shekau
“Duka kasashen nan har da Chadi sun bada gudumuwa sojoji a cikin dakarun hadin-gwiwa.”
A cewar Janar Magashi, an dauki matakan da za su magance matsalolin da za iya samu a Najeriya, ya ce za a tsare iyakoki domin a hana barkowar jama'a.
“Amma ina tabbatar maku, mu na sane da iyakokinmu, mun san da abin ke faru wa, gwamnati ta na bakin kokarinta na ganin samu zaman lafiya a Chadi.”
Kun samu labarin cewa 'dan marigayi tsohon shugaban kasa, Idris Deby, ne aka zaba domin ya gaji mahaifinsa wanda 'yan tawaye su ka hallaka a ranar Talata.
Bayan 'yan tawayen FACT sun kashe mahaifinsa, sai Sojoji su ka zabe Mahamat Debu a matsayin shugaban rikon kwarya, ana sa ran zai yi mulki na watanni 18.
Asali: Legit.ng