Tashin hankali: An tsinci gawar budurwa cikin motar basarake, ya cika wadonsa da iska

Tashin hankali: An tsinci gawar budurwa cikin motar basarake, ya cika wadonsa da iska

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Edo sun gano gawar wata budurwa mai shekaru 27 cikin motar wani basarake a jihar
  • 'Yan uwan marigayiyar sun tafi asibitin inda suka rika kuka suna neman hukuma ta bi musu hakkinsu daga basaraken
  • Daga bisani, jami'an yan sanda sun iso asbitin sun tafi da motar kirar Lexus SUV tare da gawar matar rufe a cikin motar

Edo - Hankulan mutane ya tashi a jiya a harabar asibitin kwararru na jihar Edo da ke Sapele Road a Benin yayin da aka gano gawar wata budurwa rufe cikin wani motar basarake da aka sakayya sunansa kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Faruwar lamarin ya jefa iyalan budurwar mai shekaru 27, mai suna Faith Aigbe cikin alhini.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Tashin hankali: An tsinci gawar budurwa cikin motar basarake, ya cika wadonsa da iska
Jami'in Dan Sandan Nigeria. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Yan uwa da iyalan matar da ta riga mu gidan gaskiya sun taru suna cike da bakin ciki a yayin da gawar ta ke rufe cikin motar kamar yadda rahoton na The Guardian ya bayyana.

A cewar wasu daga cikin 'yan uwan marigayiyar masu suna Mrs Janet Asemota da Mercy Eddy, sun yi ikirarin cewa basaraken ne ya kawo Faith asibitin.

Sun ce bayan ya gano ta mutu, basaraken sai ya rufe motar mai bakin gilashi kirar Lexus SUV ya kuma tsere.

Wata kawar marigayiyar da sauran 'yan uwanta sun rika sharbar kuka suna neman a bi musu hakkin su.

Yan sanda daga Aideyan sun iso wurin da abin ya faru sannan suka dauki motar tare da gawar.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

Kara karanta wannan

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel