Babu tsarin karba-karba na shugabancin kasa a kundin tsarin mulkin APC, Yahaya Bello

Babu tsarin karba-karba na shugabancin kasa a kundin tsarin mulkin APC, Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce tsarin mulkin shugabancin kasa na karba-karba ba ya cikin kundin tsarin jam’iyyar APC
  • Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin nadin shugaban wata kungiyar matasan Kaduna masu masa kamfen din shugabancin kasa
  • A cewar sa, ya na da kyau matasa su zama suke da alhakin zaben sabon shugaban kasa a shekarar 2023

Kaduna - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ta ce tsarin shugabancin kasa na mulkin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin jam’iyya mai mulki ta APC.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin taron nada shugaban wata kungiyar matasan arewa a Kaduna inda ya ce matasan Najeriya ne suke da alhakin zaben shugaban kasa.

Daily Trust ta ruwaito yadda rantsarwar kungiyar da suke kira YBN ta kasance wanda bai kai kwana 3 ba da kungiyar dattawan arewa ta NEF ta ce akwai yuwuwar arewa ta ci nasarar zaben 2023 saboda ta na da yawan da za ta iya cin zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

Babu tsarin karba-karba na shugabancin kasa a kundin tsarin mulkin APC, Yahaya Bello
Babu tsarin karba-karba na shugabancin kasa a kundin tsarin mulkin APC, Yahaya Bello. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bello wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman na harkokin matasa da dalibai, Ahmed Jubril, ya ce cigaba mai kyau ne matasan Najeriya su dinga tallafa wa 'yan uwan su wurin neman mukami babba kamar shugaban kasan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa:

“Abu mai kyau gwamna Yahaya Bello yake yi saboda akwai wasu kasashe da muka ga matasa suna jagorantar su. Cigaban mu ne matashi kamar Gwamna Bello ya zama shugaban Najeriya.”

Daily Trust ta ruwaito cewa, batun mayar da shugabanci kudu, gwamna Bello ya ce:

“Duk salon siyasa ne, kowa ya na da damar yi wa wani kamfen. Amma a matsayin mu na ‘yan jam’iyyar APC, ba mu da damar sanya wani a wani matsayi na tsawon lokaci. A bar matasa su yi yadda suke so.
“Idan har matasa suka zabi gwamna Bello a matsayin shugaba na kwarai, da izinin Ubangiji sai ya zama shugaban kasa, sai dai ka na naka Allah na na shi.

Kara karanta wannan

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

“Idan aka zabi Bello a matsayin shugaban kasa, zai dinga abubuwan sa daban saboda hakan ya kasance ya na yi. Yanzu kasar nan ta farfado daga Coronavirus kuma tattalin arziki ya yi kasa, idan kun lura jihar Kogi ita ce jihar da tafi saurin farfadowa cikin lokacin nan.
“Mun yarda da cewa Bello shi ya fi dacewa da kasar nan a halin da ake ciki,” a cewar sa.

Yayin da matasan su ka zabi shugabannin tafiyar wannan kungiyar ta su na jihohi 19 na arewa, matasan sun yi kira ga gwamnonin kudu a kan batun tsarin karba-karba inda suka ce ba ya daga cikin kundin tsarin mulki.

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

A wani labari na daban, Dan majalisa mai wakiltar mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a tarayya daga jihar Oyo a majalisar dattawa, Shina Peller, ya mayar wa dattawan arewa martani kan matsayarsu a mulkin karba karba a kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudanci

A ranar Lahadin da ta gabata, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa, ya ce arewa ba za ta zuba ido ta zama ta biyu ba a 2023, ya kara da cewa yankin ne zai samar da shugaban kasan Najeriya na gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma a wata takardar ranar Talata, Shina ya musanta cewa yawan kuri'un ba su ne ke nufin cewa za a yi burus da daidaito da adalci ba, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel