Bayan katse hanyoyin sadarwa, Fusatattun mutane sun kona gidan Kwamishinan Sokoto, sun fadi dalili

Bayan katse hanyoyin sadarwa, Fusatattun mutane sun kona gidan Kwamishinan Sokoto, sun fadi dalili

  • Wasu fusatattun matasa sun kone gidan kwamishinan tsaro na jihar Sokoto, Garba Moyi, bisa ƙin halartar taron nemo hanyoyin magance matsalar tsaro
  • Rashin zuwansa wurin taron ya fusata matasa, inda bayan ƙone gidansa, mutanen suka wuce gidan dagaci, suka farfasa masa mota
  • A kwanakin baya ne, gwamnatin Sokoto ta sanar da katse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 cikin 23 na jihar

Sokoto - Fusatattun matasa sun ƙone gidan kwamishinan tsaro na jihar Sokoto, Garba Moyi, saboda ƙin halartar taro kan yanayin tsaron yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Isa, mahaifar kwamishinan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Haka nan kuma mutanen sun kone gidan magajin garin. Amma lamarin ya faru ne yayin da kwamishinan yake babban birnin jihar.

Fusatattun mutane sun kona gidan Kwamishinan Sokoto
Bayan katse hanyoyin sadarwa, Fusatattun mutane sun kona gidan Kwamishinan Sokoto, sun fadi dalili Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kauyukan Isa, Sabon Birni, Gwaranyo, Rabah, Gada, da Tangaza, sune yankuna da yan bindiga suka matsa wa da yawaitar kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

Meyasa mutanen suka ɗauki wannan matakin?

Ɗaya daga cikin mazauna Sokoto, Abubakar Isa, ya bayyana cewa matasan sun fusata da kwamishinan da kuma sauran manyan yan siyasan yankin.

Abubakar yace:

"Wasu daga cikin mutanen sun ɗauka cewa kwamishinan ya yi watsi da mutanen asalin shi. Hare-hare sun ƙara munana kwanan nan, duk ƙoƙarin magance wa da suka ce suna yi."
"Babu ranar da zata zo ta wuce ba'a kashe wani mutum ba ko a yi garkuwa da wani a Isa da Sabon Birni."
"Fusatattun matasan sun je wurin taron suka gano kwamishinan bai samu halarta ba, daga nan suka wuce gidansa suka cinna wuta, kafin daga bisani suka ƙarisa gidan dagaci, suka farfasa motarsa."

Gwamnatin Sokoto ta katse hanyoyin sadarwa

Gwamnatin jihar Sokoto ta katse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 cikin 23 dake faɗin jihar domin dakile ayyukan yan bindiga.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin matasa, an harbe fasto yayin da yake tsaka da ibada

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Sanusi Abubakar, ya tabbatar da ƙone gidan kwamishinan ga jaridar Premium times.

A wani labarin na daban Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rogo da Karaye, Haruna Isah Dederi, ya koka kan shigar yan bindiga jihar Kano .

A cewarsa yan bindigan dake gudowa daga luguden wutan rundunar sojoji a Zamfara da Katsina sun fara kai hari ƙaramar hukumar Rogo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel