Kada ku tausayawa yan bindiga, ku buɗe musu wuta ko sun shiga cikin mutane, Gwamnan Arewa ya hasala

Kada ku tausayawa yan bindiga, ku buɗe musu wuta ko sun shiga cikin mutane, Gwamnan Arewa ya hasala

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bukaci jam'an soji kada su sassauta wa yan bindiga a ko ina suka gamu
  • Masari ya roki sojojin su buɗewa yan bindiga wuta koda sun shiga cikin mutane, amma su ɗauki mataki dan kada a kashe mutane da yawa
  • Masari ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin ministan labaru, Lai Muhammed, wanda ya zo jin yadda take wakana

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya roki sojoji kada su tausaya wa yan bindiga ko ina suka gansu, su buɗe musu wuta, kamar yadda Amniya Hausa ta ruwaito.

Gwamnan yace matakan da aka ɗauka sun jefa rayuwar yan bindigan cikin mawuyacin hali, inda a yanzun suke ƙoƙarin shigowa cikin mutane.

Kara karanta wannan

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Amma Masari ya bukaci dakarun sojojin kada su tausaya musu koda sun shiga cikin mutane a bude musu wuta, ko da hakan zai ritsa da mutanen da ba ruwansu.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari
Kada ku tausayawa yan bindiga, ku buɗe musu wuta ko sun shiga cikin mutane, Gwamnan Arewa ya hasala Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai Masari ya roki jami'an sojin su ɗauki wasu matakan kariya ga mutanen idan irin haka ta faru, gudun kashe waɗanda ba ruwansu da yawa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Masari ya yi wannan furucin ne yayin da ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ziyarce shi, domin samun bayanai kan irin nasarorin da ake samu a yaƙi da yan bindiga.

Ba maganar sulhu da yan ta'adda

A nasa ɓangaren, Ministan yace:

"Daga yanzun gwamnatin tarayya ba zata amince da yin sulhu da yan bindiga da yan ta'adda ba."

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, yace ba dai-dai bane tattaunawar sulhu da irin waɗannan mutanen.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

"Waɗannan mutanen ba su da addini, ya kamata a haɗa karfi da karfe kuma a ɗauki duk matakan da ya dace domin kawar da su baki ɗaya."

A wani labarin na daban kuma Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rogo da Karaye, Haruna Isah Dederi, ya koka kan shigar yan bindiga jihar Kano.

A cewarsa yan bindigan dake gudowa daga luguden wutan rundunar sojoji a Zamfara da Katsina sun fara kai hari ƙaramar hukumar Rogo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel