Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon mataimakin gwamnan CBN da ya rasu
A yau ne aka samu mummunan labarin mutuwar wani jigo a Najeriya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailfaia. Ya taka rawa a Najeriya ta fuskoki da dama.
A cikin wannan rahoton nan, Legit.ng ta kawo muku wasu abubuwa da kuke bukatar sani game da Dr Obadiah Mailafia.
Bayanai kan Dr Obadiah Mailafia
1. Ya kasance tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
2. Ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2019.
3. An haifi Mailafia a ranar 24 ga Disamba, 1956, a Karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.
4. Ya kammala digirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, a shekarar 1978 inda ya karanta kimiyyar zamantakewa (Siyasa, Tattalin Arziki, da Ilimin zamantakewa).
5. Ya kuma yi digiri na biyu a fannin na tattalin arziki.
6. Ya tafi zuwa kasar Ingila, Kwalejin Oriel, inda ya sami digirin digirgir daga Jami'ar Oxford a 1995.
7. Ya shiga harkar siyasa a shekarar 2018 sakamakon karuwar kashe-kashe a Kudancin Kaduna.
8. Ya taba zargin wani gwamnan arewa cewa shine kwamandan Boko Haram.
9. Biyo bayan furucinsa kan Boko Haram, hukumar DSS ta gayyace shi ofishinta
10. Daga baya ya lashe amansa
Tsohon mataimakin gwamnan CBN, mai sukar Buhari ya rasu
A wani labarin, Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya rasu.
Har yanzu ba a samu cikakkun bayanai game da mutuwar tasa ba, amma majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.
Mailafia ya kasance mai tsananin sukar gwamnatin Buhari, ya kuma taba tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019 a karkashin jam'iyyar ADC.
Asali: Legit.ng