Ku Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda Idan Ba Kare Su Kuke Yi Ba, PDP Ga Fadar Shugaban Kasa

Ku Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda Idan Ba Kare Su Kuke Yi Ba, PDP Ga Fadar Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnatin shugaban ƙasa Buhari da kokarin bada kariya ga masu ɗaukar nauyin ta'addanci
  • PDP ta faɗi haka ne yayin martani ga kalaman fadar shugaban ƙasa cewa FG ba zata fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ba, zata maida hankali wajen hukunta su
  • Kakakin PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, yace matakin FG ya nuna karara cewa mutanen suna da alaƙa da jam'iyyar APC

Abuja - Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin Buhari da kokarin kare masu ɗaukar nauyin yan ta'adda da yan bindiga a ƙasar nan, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

PDP ta faɗi haka ne yayin da take martani kan kalaman kakakin shugaban ƙasa, Femi Adesina, cewa gwamnatin tarayya ba ta da ra'ayin fallasa da kuma kunyata masu ɗaukar nauyin yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

Kola Ologbondiyan
Ku Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda Idan Ba Kare Su Kuke Yi Ba, PDP Ga Fadar Shugaban Kasa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Me FG take shirin yi?

Da yake fira da kafar watsa labarai ta Channels TV, Adesina yace maimakon fallasa sunayen gwamnatin tarayya zata maida hankali wurin gurfanar da su domin a hukunta su.

Wannan dai yazo ne bayan haɗaɗɗiyar daular larabawa (UAE) ta saka yan Najeriya shida a jerin yan ta'adda.

Da yake maida martani a wani jawabi, kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yace gwamnatin Buhari ta gaza kawo karshen ayyukan ta'addanci a faɗin ƙasa.

Dagaske gwamnati na kare yan ta'adda?

Wani sashin jawabin yace:

"Ƙin fallasa sunayen masu hannu a ayyukan ta'addanci da gwamnatin Buhari ta yi, ya nuna ƙarara cewa tana kokarin kare yan ta'adda da yan bindiga ne da suka addabi yan ƙasa."
"Matsayar PDP a bayyane take game da kalaman gwamnatin Buhari cewa ba zata fallasa sunayen mutanen ba, sunayen mutun 6 da UAE ta turo mata masu ɗaukar nauyin ta'addanci."

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa da Ya Haifa Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

"Matakin gwamnatin APC na ƙin fitar da bayanan waɗannan mutanen duk da yawaitar aikata manyan laifuka na kashe-kashe, satar mutane, cin zarafin mata, ya nuna matsayar PDP ƙarara cewa waɗannan mutanen suna da alaƙa da APC."

A wani labarin na daban kuma Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya Sun Yi Dana Sanin Daukar Makamai, Sun Fadi Dalilinsu

Tubabbun yan ta'addan sun bayyana haka ne yayin da manema labarai suka kai ziyara ɗaya daga cikin wuraren da ake tantance masu miƙa wuya a Borno ranar Talata.

Ɗaya daga cikin mayaƙan da suka mika wuya yace kwamandojinsu sun yaudare su kan dalilin da yasa suka ɗauke su aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262