Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da wani Ɗan Kasuwa a Jalingo

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da wani Ɗan Kasuwa a Jalingo

  • Miyagun yan bindiga sun sace wata mata dake shayarwa tare da wani ɗan kasuwa da mutum ɗaya a Jalingo
  • Rahoto ya nuna cewa yan bindiga aƙalla 10 ne suka farmaki yankin da tsakar dare inda suka sace mutanen uku
  • Mutanen yankin sun bayyana matukar damuwarsu bisa ƙin ɗaukar mataki kan maharan da jami'an tsaro suka yi

Jalingo, Taraba - Yan bindiga sun sace wata mata dake shayarwa tare da wasu mutum biyu a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa maharan waɗanda suka kai adadin 10 sun mamaye yankin da tsakiyar daren ranar Lahadi, inda suka sace mutanen.

Maharan sun yi awon gaba da matar ne biyo bayan rashin ganin mijinta, wanda ake zargin shine abin harinsu.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Mutum 6 Sun Mutu Yayin da Miyagun Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari Sokoto

Daga nan ne sai miyagun suka fasa wani gida dake kusa da nan, inda suka sace wani ɗan kasuwa da ɗan uwansa ɗaya.

Yan bindiga sun sace mutum uku a Taraba
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da Wani Ɗan Kasuwa a Jalingo Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan mutane sun hana wasu miyagu sace mutane a yankin asibiti na musamman dake Jalingo.

Yan bindiga sun takurawa yankin

Yankin da lamarin ya faru, wanda yake kusa da dutse, kan hanyar Mallam Audu-Pantisawa, miyagun sun maida shi tamkar gidan su.

Wasu mazaunan yankin da aka tattauna da su, sun nuna matukar damuwarsu kan halin ko in kula da kuma ƙin ɗaukar mataki kan maharan da hukumomi suka yi.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, yace yana cikin taro ne amma zai bada amsa idan ya fito.

Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton kakakin yan sandan bai kira ba kuma bai fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

A wani labarin kuma rundunar soji ta bayyana irin tasirin da addu'o'in yan Najeriya ƙe yi a yaƙi da Boko Haram

Kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai, Christopher Musa, yace addu'ar yan Najeriya ce take sa mayakan Boko Haram miƙa wuya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Musa yace sojoji sun samu gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da yan ta'addan Boko Haram da kuma ISWAP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262