Dalibin da ke zuwa makaranta a kan keke duk ruwa duk iska ya samu tallafin mutumin kirki

Dalibin da ke zuwa makaranta a kan keke duk ruwa duk iska ya samu tallafin mutumin kirki

  • Wani dalibin mai kwazon zuwa makaranta ya sami tallafi daga wasu mutanen kirki a jihar Kano
  • A kwanakin baya hoton dalibin ya shahara a kafar Facebook, inda mutane da dama suka nuna son taimaka masa
  • A halin yanzu, wani mutum ya yi alkawarin gwangwaje dalibin da kyautuka masu daraja don bashi kwarin gwiwa

Wani dalibin da labarin jarumtarsa ya yadu a kafafen sada zunumta cikin makwannin nan da suka gabata ya sami tallafin wani mutumin kirki; Ibrahim Sanyi-Sanyi inda ya ba shi gudummawa ta kudade masu tsoka.

A wani rubutu da Ibrahim ya buga a ranar Asabar, 18 ga Satumba, ya bayyana cewa an gano dalibin mai suna Mallam M. bayan bin diddiginsa, wanda ke zuwa makaranta a kan keke duk tsananin ruwa duk tsananin iska.

Dalibin da ke zuwa makaranta a kan keke duk ruwa duk iska ya samu tallafin mutanen kirki
Hotunan dalibin da ya samu tallafi daga Ibrahim Sanyi-sanyi | Hoto: Ibrahim Sanyi-Sanyi
Asali: Facebook

Zan ba shi N100,000

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Sanyi-Sanyi ya bayyana cewa dalibin yana sakandare ajin SS1 a Makarantar Sakandaren Larabci ta Gwamnati da ke Kura kuma yana tahowa ne daga kauyensu zuwa makaranta kowace rana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda haka, ya kara da cewa zai ba da gudummawar N100,000, jakar makaranta, da sauran kayan makaranta ga dalibin.

Sanyi-sanyi ya kuma yi kira ga wasu da ke da sha'awar ba da gudummawa ga dalibin da cewa kofa a bude take.

Martanin jama'a kan wannan aiki na Ibrahim Sany-sanyi

Mutane da yawa a kafar Facebook sun yi martani kan wannan kyakkyawan aiki, duba kaga martaninsu.

Salisu Ibrahim Sheriff ya ce:

"Masha Allah. Zan aiko nawa gudummawa ta akwatin sakonka. Allah ya amfanar dashi akan karatunsa. Amin."

Hussaini Najiddah Umar ya yi martani da cewa:

"Masha Allah abinda Ibrahim yayi abu ne mai kyau. Allah Ya saka masa da alheri. Ina ba da shawarar masu so su taimaka su fara taimakawa yara a unguwanninsu domin akwai irin wadannan yaran da suke kokari wajen neman ilimi, kuma suna bukatar taimakon. Allah ya ba da ikon taimakawa."

Kara karanta wannan

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

Lawal Umar Faruk yace:

"Oga Sanyi-Sanyi, kai abin koyi ne ga da yawanmu. Allah ya albarkace ka, dukiyar ka da dangin ka. Allah Ya karbi duk abin da kake yi na Ibadat."

MB Mahmoud yace:

"Wato Sanyi-Sanyi kai ma Allah Ya sanyaya ma."

Abdulrazak Ibrahim yace:

"Abin mamaki Na halarci wannan makarantar na tsawon shekaru 3. Ta ina zan aiko da gudummawata?"

Hussaini Ubali yace:

"Ikon kafafen sada zumunta kenan, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi Mallam."

Rochas: Aikin sanata ya fi karfin albashin N13m duk wata, muna bukatar kari

A wani labarin, Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ce kusan Naira miliyan 13 da kowanne sanata ke samu a matsayin albashi da alawus-alawus bai kai wahalar aikin da 'yan majalisar ta dattawa ke yi ba.

Rochas wanda shi ma dan majalisar dattawa ne ya yi magana ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba a Abuja, in ji rahoton The News.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

Tsohon gwamnan na Imo wanda ke gardama kan ya kamata a rage yawan sanatoci da aka zaba daga kowace jiha zuwa uku ya ce albashin sanata ya kai kimanin naira miliyan biyu tare da alawus na gida na naira miliyan uku da sauran alawus na kusan miliyan 11.

Asali: Legit.ng

Online view pixel