Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya aike da wasika ga majalisar dattijai, ya bukaci yin garambawul a PIA

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya aike da wasika ga majalisar dattijai, ya bukaci yin garambawul a PIA

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattijai ta yi garambawul a sabuwar dokar man fetur (PIA)
  • A wasikar da ya aike wa sanatocin ranar Talata, Buhari ya nemi majalisar ta zare ministoci biyu daga mambobin kwamitin zartarwa na NNPC
  • Hakazalika shugaban ya bukaci sanatocin su tantance mambobin majalisar zartarwa ta hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike da bukatar yin garambawul a sabuwar ma'aikatar man fetur, PIA, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wasikar da ya aike majalisar, Buhari ya bukaci a gyara sabuwar dokar man fetur ɗin domin cire ma'ikatar albarkatun man fetur da ma'aikatar kuɗi daga NNFC.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya aike da wasika ga majalisar dattijai, ya bukaci yin garambawul a PIA
Asali: Instagram

Shugaban ya bayyana cewa idan aka cire ministocin biyu, zasu samu damar gudanar da ayyukan ma'aikatar su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure dan hadimin gwamna Tambuwal shekaru 4 a magarkama bisa laifin yada bidiyon batsa

Buhari ya bukaci a ƙara mambobi

A cikin takardar, wacce shugabaan majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zaman majalisar na yau Talata, Buhari ya bukaci a ƙara mutane a majalisar kula da NNPC daga biyu zuwa shida.

"Wanna garambawul ɗin zai samar da wakili da kuma gudummuwa daga kowane ɓangare na ƙasar nan wajen yanke hukunci a babban ma'aikata kamar ma'aikatar man fetur."
"Ma'ikatu biyu suna da ayyukan da tsarin mulki ya tanadar musu, zasu samu damar gudanar da ayyukansu ba tare da kasancewa a ciki mambobin ba."

Sai dai shugaban ya bukaci waɗanda za'a ƙara ɗin kada su kasance cikin yan majalisar zartarwa na ƙasa, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Hakazalika, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike wa majalisar dattijai wasika, yana bukatar su tantance mambobin da ya naɗa a majalisar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC).

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya aika wa 'Yan Majalisa takarda, ya yi sababbin nadin mukamai a EFCC

A wani labarin kuma Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal , shine ya sanar da haka a wata fira da gidan Radiyo na VOA Hausa, ranar Litinin.

Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu amincewar ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, kafin ta tabbatar da datsewar ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel