Da Duminsa: Mutum daya ya mutu, wasu da dama sun ɓata yayin da wani babban gini ya danne mutane a Ondo

Da Duminsa: Mutum daya ya mutu, wasu da dama sun ɓata yayin da wani babban gini ya danne mutane a Ondo

  • Wani gini da ya faɗo a yankin Akure, babban birnin jihar Ondo, ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata guda ɗaya
  • Wasu mutane da dama rushewar ginin ya ritsa da su, amma mutanen dake kewayen yankin sun fara ƙoƙarin ceto su
  • Ɗaya daga cikinn 'ya'yan matar da ginin ya hallaka, ya zargi mai gidan da sanadin rushewar

Ondo - Rahotanni sun nuna cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wani gini ya ruguzo wa mutane a yankin Fanibi dake Akure, babban birnin jihar Ondo, ranar Talata da safe.

Punch ta ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen dake zaune a wurin sun maƙale a ciki yayin da mutanen yankin suka fara ƙoƙarin ceto su.

Wani shaidan gani da ido yace wata mata ce ta rasa rayuwarta, kuma har zuwa yanzun ba'a gano bayanai game da ita ba.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa da Ya Haifa Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

Wani gini ya rushe a Ondo
Da Duminsa: Mutum daya ya mutu, wasu da dama sun ɓata yayin da wani babban gini danne mutane a Ondo Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mutane sun kai gawar matar zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin dake yankin kafin a gano yan uwanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya jawo rushewar ginin?

Ɗaya daga cikin ƴaƴan matar da rushewar ginin ya yi ajalinta, Fasto Benson Olom, ya zargi mai gidan da jawo rushewar ginin.

Olom, wanda matarsa da 'ya'yansa 5 suka tsira daga lamarin, ya shaidawa Vanguard cewa lokacin da mai gidan ya yi ƙoƙarin gyara ginin, sai da ya gargaɗe shi.

Yace:

"Sai da na gargaɗe shi kan gyaran ginin nan domin zai rage ƙarfin ginin amma sam ya ƙi saurare na."
"Shi abinda yake hange kawai shine yadda zai samu kuɗaɗe sosai bayan ya sake gina ɗakuna da falo."
"Ni da matata da kuma ƴaƴan mu hudu, mun tsira ba tare da jin wasu raunuka ba, mutum ɗaya daga cikin 'ya'yana ne ya samu rauni a kansa, amma an kai shi asibiti."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da Wani Ɗan Kasuwa a Jalingo

A wani labarin kuma Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal , shine ya sanar da haka a wata fira da gidan Radiyo na VOA Hausa, ranar Litinin.

Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu amincewar ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, kafin ta tabbatar da datsewar ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel