Sojojin Najeriya sun sheke 'yan fashin daji 42 a yankin Shiroro da ke jihar Niger

Sojojin Najeriya sun sheke 'yan fashin daji 42 a yankin Shiroro da ke jihar Niger

  • Jami'an tsaro da suka hada da sojoji tare da 'yan sanda sun halaka 'yan fashin daji 42 a Alawa da ke Shiroron jihar Neja
  • Jami'an tsaron sun tare 'yan bindigan a Maganda yayin da suka tattaro daga jihar Zamfara inda sojoji ke musu lugude
  • Yayin artabun, an rasa ran soja daya, wasu sun samu rauni kuma an samo makamai, babura da shanun sata

Niger - Jami'an tsaron Najeriya da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun sheke miyagun 'yan fashin daji 42 a yankin Alawa da ke Shiroro a jihar Neja.

PRNigeria ta tattaro cewa, jami'an tsaron hadin guiwar sun kai wa 'yan bindigan samame yayin da suka gudo daga jihar Zamfara inda sojoji suka matsa musu da luguden wuta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

Wata majiya da ke da hannu cikin aikin ta sanar da PRNigeria cewa, sakamakon musayar wutan da aka yi, soja daya ya rasa rayuwarsa yayin da wani ya samu rauni.

Sojojin Najeriya sun sheke 'yan fashin daji 42 a yankin Shiroro da ke jihar Niger
Sojojin Najeriya sun sheke 'yan fashin daji 42 a yankin Shiroro da ke jihar Niger. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Sojojin sun samu bayani na musamman kan kaiwa da kawowar 'yan bindiga ta wurin Alawa.
"Sun tsero daga luguden da sojojin da ke musu a dajikan Zamfara, inda mu kuma muka ci karo da su a wuraren Manganda. A kalla 'yan fashin daji 42 ne suka sheka lahira yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika.
"Mun rasa soja daya, yayin da wasu sojojin suka samu raunika inda aka kai su asibitin Asmau da ke Kagara.
“Mun samo miyagun makamai, babura da kuma shanun sata daga 'yan bindigan yayin samamen," ya bayyana.

Dalilin da yasa gwamnoni ke tsoron sa hannu kan hukuncin kisa, Ganduje

Kara karanta wannan

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnoni na matukar tsoron sa hannu kan hukuncin kisa saboda ba za su so bayan kaddamar da hukunci ba daga baya a gane cewa wanda aka kashen bai dace da hukuncin ba.

An dade ana caccakar Gwamnonin kasar nan kan jinkirin da suke yi wurin sa hannu kan aiwatar da wasu hukunce-hukuncen kotu, lamarin da ake alakanta shi da dalilin cikar gidajen gyaran hali a fadin kasar nan.

Amma a yayin amsa tambayar da Trust TV ta yi wa Gwamna Ganduje a wata tattaunawa, ya ce sun tsoron sa hannu kan hukuncin kisa saboda da yawa daga cikin tsarin shari'a "abun zargi ne."

Asali: Legit.ng

Online view pixel