Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

  • Majalisar wakilai ta nemi wani kwamiti da ya tabbatar da hada rahoto kan kudaden da gwamnati ta kwato
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da karbo kudaden da shugabanni suka tsallaka dasu
  • Hakazalika, majalisar ta nemi a ba ta rahoto kan kadarorin da gwamnatin Buhari ta sayar da wadanda za ta sayar

Abuja - Majalisar wakilai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ta nemi Kwamitin Aiwatarwa ta Shugaban Kasa (PIC) kan kadarorin da filaye mallakar gwamnati da su gabatar da rahotannin dukkan kadarorin da aka kwace daga tsoffin shugabannin Najeriya.

'Yan majalisar sun fi mayar da hankali musamman kan Janar Sani Abacha wanda Gwamnatin Najeriya ta kwato kaddarori da kudade da dama daga turai da aka ce mallakinsa ne, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

Dan majalisar wakilai Ademorin Kuye, shugaban kwamitin wucin gadi kan kadarorin da aka yi watsi da su ya ce majalisar tana bukatar rahoton dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun shugabanni, musamman Janar Abacha.

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka
Majalisar wakilai | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Ya fadi haka ne lokacin da Babban Sakataren PIC ya bayyana a kwamitin a babban birnin tarayya Abuja.

A baya, jaridar TheCable ta ruwaito adadin kudaden da aka kwato daga turai wadanda aka yi amannar cewa, Abacha ne ya tsallaka dasu.

A cewar Mista Kuye:

"Muna bukatar sanin yanayin kadarorin sannan kuma mu san ko kadarorin suna dauke da shaidar mallakar wani.

Majalisa ta nemi rahoton kadarorin da Buhari ya sayar da wadanda zai sayar na gwamnati

Kwamitin ya kuma nemi bahasi game da sayar da kadarorin Gwamnatin Tarayya da PIC ke lura da su.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

Mista Kuye ya ce kwamitin ya gano wasu kaddarorin da PIC ta yi ikirarin ta sayar wadanda ba a sayar da su ko kuma ba a biya kudadensu ba sabanin ikirarin na PIC.

Ya umarci PIC da ta ba kwamitin rahotanni cikakku kan kadarorin Gwamnatin Tarayya da aka sayar, adadin da aka samu daga siyarwar, wadanda har yanzu ba za a siyar ba da wadanda ake jira.

Mista Kuye ya kuma shaidawa PIC dole ne ta bayyana adadin kudaden da aka tura wa Gwamnatin Tarayya daga siyarwar tare da shaidar aika kudin ga gwamnati.

Ya kara da cewa duk kadarorin da aka nuna wa kwamitin amma ba a sanya a cikin rahoton farko ba ya kamata a tura wa kwamitin majalisar wakilai.

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

A wani labarin, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce gwamnatin Buhari ba ta da sha’awar bayyana suna da kunyatar da masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

Adesina ya fadi haka ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels.

A makon da ya gabata, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanya 'yan Najeriya shida cikin jerin 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel