Peter Obi ga Buhari: Ka dinga daukan hoto da 'yan Najeriya masu tasiri, ba 'yan siyasa marasa daraja ba

Peter Obi ga Buhari: Ka dinga daukan hoto da 'yan Najeriya masu tasiri, ba 'yan siyasa marasa daraja ba

  • Peter Obi, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa ya caccaki shugaban kasa Buhari kan daukan hoto da masu sauya sheka
  • Tsohon gwamnan jihar Anambaran ya ce bai dace Buhari ya dinga daukan hoto da 'yan siyasa marasa tausayi da jin kai ba
  • A cewarsa, gara Buhari ya dinga hotuna a jana'izar sojoji da 'yan sanda tare da iyalansu da kuma 'yan kasa masu tasiri

Anambra - Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daina daukar hotuna da 'yan siyasa marasa tausayi da daraja da ke sauya sheka.

Wasu fitattun 'yan siyasa sun bar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma sun gana da shugaban kasan a Aso Rock inda suka dauki hotuna.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Manyan mukamai da Fani-Kayode zai iya samu a matsayin tukwicin sauya sheka zuwa APC

Peter Obi ga Buhari: Ka dinga daukan hoto da 'yan Najeriya masu tasiri, ba 'yan siyasa marasa daraja ba
Peter Obi ga Buhari: Ka dinga daukan hoto da 'yan Najeriya masu tasiri, ba 'yan siyasa marasa daraja ba. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Femi Fani-Kayode a makon da ya gabata ya sanar da sauya shekar da yayi zuwa jam'iyya mai mulki kuma ya dauka hotuna yayin da ya gana da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.

Obi a wata tattaunawa da Arise TV a ranar Litinin, ya kushe yayin da ake yi inda ya kara da cewa babbar alamar da ke nuna cewa za ka iya zama komai kuma za ka iya zuwa ko ina kenan.

Ya ce kamata shugaban kasa ya dinga daukan hoto a jana'izar sojoji da 'yan sandan da suka mutu tare da iyalansu ko kuma da matasan da ke aikin kirkire-kirkire.

"Bari in fada muku, abinda na ke gani ya na ba ni mamaki kan yadda ake sauya sheka a yau. A kowacce rana ana jagorantar jama'a domin su ga shugaban kasa kuma su dauka hoto. Ina damuwa da hakan.

Kara karanta wannan

Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji

"Ina son ganin shugaban kasan ya na daukan hoto a jana'izar sojoji ko 'yan sanda da suka rasu tare da iyalansu," tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasan yace.
"Ina son ganin shi ya na daukan hoto da matasa wadanda ke kirkire-kirkire a masana'antun fasaha. Ina son in ga ya na daukan hoto da jama'a masu tasiri ba 'yan siyasa marasa tausayi da daraja ba."

Hakeem Baba Ahmed: Ba tashi duniya za ta yi ba idan aka sake zaben dan arewa shugaban kasa

A wani labari na daban, kakakin kungiyar dattawan arewa, NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ba tashi duniya za ta yi ba idan aka sake zaben dan arewa a matsayin shugaban kasar Najeriya.

A yayin jaddada cewa 'yan arewa ne suka fi yawa a kasar nan, ya ce arewa ba za ta amince da zama ta biyu ba a 2023, yayin da yankin ya ke da yawan da zai iya kwace mukamin farko, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

Ya sanar da hakan yayin da ya ke jawabi a taron shugabanci na farko na Maitama Sule wanda daliban CNG suka shirya a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin ranakun karshen mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel