Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji

Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji

  • Shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya ce daga yanzu duk farmakin da aka kai bariki, kwamanda za a kama da laifi
  • Faruk Yahaya ya sanar da cewa ya zama dole kwamandoji su dage tare da tabbatar da tsaro a sansaninsu ko kuma barikinsu
  • Ya kara da cewa, hakki ne na shugaba ya kasance mai nagarta tare da kwarewa wurin shugabantar wadanda ke kasansa

FCT, Abuja - Laftanal Janar Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa, ya ce duk wani farmaki da aka kai bariki, babu shakka kwamandan barikin zai kama da laifi.

Ya sanar da hakan ne yayin rufe taron shugaban sojin kasa da aka yi, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban sojin kasan ya yi kira ga kwamandoji da su tabbatar da cewa sun kasance a shirye kuma suna sa ido a kowanne lokaci domin guje wa farmakin ba-zata.

Kara karanta wannan

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji
Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da cewa, halin baya-baya a bangaren wasu kwamandoji abu ne da ba zai lamunta ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina son tunatar da shugabanni da kwamandoji kan bukatar su tabbatar da isasshen tsaro a sansaninsu da barikinsu. Kwamandoji za mu kama da alhakin duk wani matsalar tsaro.
"Amfanin shugabanci nagari ya na da yawa ballantana a rundunar soja. Ya zama wajibi ga shugaba da ya tabbatar da cewa mabiyansa sun yarda da shi. Ana gina yarda ne da halaye nagari wanda su ne jigon shugabanci na gari kuma ta haka ake samun sakamako mai kyau.
"A don haka, kwamanda a kowanne mataki ya zama wajibi ya samar da ingantaccen shugabanci mai kyau yayin da ya ke kokarin kiyaye dukkan dokokin rundunar sojin.
"Dole ne kwamandoji su tabbatar da cewa sun dage tare da gina mutuntawa da yarda a zukatan mabiyansu. Na umarci dukkan shugabanni da su fitar da tsarin shugabanci kuma su yi amfani da shi wurin horar da na kasa da su domin tabbatar da aiki na tafiya daidai."

Kara karanta wannan

Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta

Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

A wani labari na daban, majalisar jihar Kano ta amince wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya karbo bashin N4 biliyan da ya ke nema domin kammala ayyukan wutar lantarki na Tiga da Challawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an amince da karbo bashin ne yayin zaman majalisar wanda ya samu shugabancin kakakin majalisar jihar Kano, Ibrahim Chidari.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da aka mika wa daraktan yada labarai na majalisar, Uba Abdullahi, wanda ya ce majalisar ta zauna kan al'amarin bayan kakakin ya karantowa majalisar da gwamnan ya tura musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel