Hakeem Baba Ahmed: Ba tashi duniya za ta yi ba idan aka sake zaben dan arewa shugaban kasa
- Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa, ya ce duniya ba tashi za ta yi ba idan an ba dan arewa shugabancin kasa
- Kamar yadda ya sanar yayin jawabi a taron shugabanci da CNG ta shirya na Maitama Sule, ya ce 'yan arewa ba za su zama na biyu a kasar nan
- Ya jaddada cewa, 'yan arewa sun fi yawa kuma su za su cigaba da jagorancin kasar nan, wanda bai so haka ba, ya tattara ya bar kasar a 2023
Zaria, Kaduna - Kakakin kungiyar dattawan arewa, NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ba tashi duniya za ta yi ba idan aka sake zaben dan arewa a matsayin shugaban kasar Najeriya.
A yayin jaddada cewa 'yan arewa ne suka fi yawa a kasar nan, ya ce arewa ba za ta amince da zama ta biyu ba a 2023, yayin da yankin ya ke da yawan da zai iya kwace mukamin farko, Daily Trust ta ruwaito.
Ya sanar da hakan yayin da ya ke jawabi a taron shugabanci na farko na Maitama Sule wanda daliban CNG suka shirya a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin ranakun karshen mako.
Ya ce:
"Arewa ba ta siyarwa ba ce kuma 'yan arewa za su baiwa masu jerin jiran 2023 mamaki da kuma masu tunanin za su ba su kudi domin siyan kuri'unsu.
Ya ce duk wanda ba ya son dan arewa ya zama shugaban kasa, toh ya tattara komatsansa domin barin kasar idan hakan ta tabbata, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kara da kira da daliban da su kasance masu alfahari da kansu, inda ya ce kada su yadda a kwace iko daga hannunsu a kasar su ta kansu.
"Za mu jagoranci Najeriya kamar yadda muka jagorance ta a baya, ko mu ne ke shugabancin kasa ko mataimakin, za mu jagorance ta. Mu ke da yawancin kuri'un kuma damokaradiyya ta ce a zabi wanda ake so.
"A kan me za mu amince mu zama na biyu bayan mun san za mu iya siyan fom tare da takarar zama na farko kuma mu yi nasara?
"Me yasa wasu ke son yi mana barazana tare da tsorata mu? Za mu samu wannan ikon amma kan mu a kasa saboda iko daga Ubangiji ya ke. Mun gaji shugabancin, kuma wawa ba mahaukaci ba ne.
"Mun shirya wa wannan, za mu duba kalubalen tattalin arzikinmu kuma mu gyara shi. Mu kadai ne za mu iya gyara arewacinmu. A saboda wannan dalilin, ba za mu siyar da yankinmu ba. Muna gina arewaci kuma za mu cigaba da ginata daga 2023.”
Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya
A wani labari na daban, iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.
Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna, Daily Trust ta ruwaito.
Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.
Asali: Legit.ng