Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga
- Jami'an 'yan sanda masu murabus na jihar Kaduna sun fito zanga-zangar lumana ga hukumar fansho
- Tsofaffin 'yan sanda sun yi tattaki zuwa hedkwatar rundunar 'yan sanda da ke Kaduna domin mika kokensu
- Sun dade suna korafin yadda hukumar fansho ke nuna musu mugunta tare da rashin tausayi wurin rike musu kudi
Kaduna - 'Yan sandan da suka yi murabus sun fita zanga-zangar lumana kan rike musu kudade da hukumar fansho ta jihar Kaduna ta yi a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.
Jami'an sun yi tattaki har zuwa hedkwatar rundunar 'yan sandan jihar Kaduna domin mika kokensu inda suka jaddada cewa ba su da ra'ayin abinda suka kwatanta da "hukumar kisa".
A na tsawon wani lokaci, jami'an 'yan sanda a kasar nan suna ta kushe hukumar fansho.
Ga wasu daga cikin hotunan masu zanga-zangar:
Hakeem Baba Ahmed: Ba tashi duniya za ta yi ba idan aka sake zaben dan arewa shugaban kasa
A wani labari na daban, kakakin kungiyar dattawan arewa, NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ba tashi duniya za ta yi ba idan aka sake zaben dan arewa a matsayin shugaban kasar Najeriya.
A yayin jaddada cewa 'yan arewa ne suka fi yawa a kasar nan, ya ce arewa ba za ta amince da zama ta biyu ba a 2023, yayin da yankin ya ke da yawan da zai iya kwace mukamin farko, Daily Trust ta ruwaito.
Ya sanar da hakan yayin da ya ke jawabi a taron shugabanci na farko na Maitama Sule wanda daliban CNG suka shirya a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin ranakun karshen mako.
Asali: Legit.ng