Dalilin da yasa gwamnoni ke tsoron sa hannu kan hukuncin kisa, Ganduje

Dalilin da yasa gwamnoni ke tsoron sa hannu kan hukuncin kisa, Ganduje

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce gwamnoni suna tsoron sa hannu kan hukuncin kisa
  • A cewar gwamnan, suna tsoron sa hannu ne gudun a kashe mutum kuma a gane bai cancanci hukuncin ba
  • Ya tabbatar da cewa, ana yawan samun matsala a cikin hukunci, don haka suke bada umarnin a sake dubawa

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnoni na matukar tsoron sa hannu kan hukuncin kisa saboda ba za su so bayan kaddamar da hukunci ba daga baya a gane cewa wanda aka kashen bai dace da hukuncin ba.

An dade ana caccakar Gwamnonin kasar nan kan jinkirin da suke yi wurin sa hannu kan aiwatar da wasu hukunce-hukuncen kotu, lamarin da ake alakanta shi da dalilin cikar gidajen gyaran hali a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

Dalilin da yasa gwamnoni ke tsoron sa hannu kan hukuncin kisa, Ganduje
Dalilin da yasa gwamnoni ke tsoron sa hannu kan hukuncin kisa, Ganduje. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Amma a yayin amsa tambayar da Trust TV ta yi wa Gwamna Ganduje a wata tattaunawa, ya ce sun tsoron sa hannu kan hukuncin kisa saboda da yawa daga cikin tsarin shari'a "abun zargi ne."

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya tuna wani lamari da ya hada da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya ce,

"Akwai wani lokaci da ya saka hannu kan hukuncin kisa kuma aka kashe mutumin. Daga bisani, an gano cewa bai dace a kashe shi ba. Hukuncin ya na da matsala."

Ya ce bayan faruwar lamarin, gwamnoni sun kara kiyayewa wurin sa hannu kan hukuncin kisa, inda ya kara da cewa:

"Lokaci zuwa lokaci muna saka hannu, amma idan muka yi tunanin cewa ya dace a sake duba lamarin domin sake bincike, da yawa mu kan gano cewa bai dace a kashe su ba. Idan kuma aka kashe, ba za a iya dawo da rayuwa ba."

Kara karanta wannan

Bidiyon katon din giya 3,600 da Hisbah ta kama an ɓoye cikin buhunan abincin kaji a Kano

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

A wani labari na daban, iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.

Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna, Daily Trust ta ruwaito.

Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.

Asali: Legit.ng

Online view pixel