Makiyayi da shugaban Fulani sun sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kai farmaki Kaduna

Makiyayi da shugaban Fulani sun sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kai farmaki Kaduna

  • Gagararrun 'yan bindiga sun kai farmaki a yankunan karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranar Juma'a
  • Rahotanni sun bayyana yadda suka shiga har gida suka dauka shugaban Fulanin Lere kuma suka harbe shi
  • An gano cewa, sun kara da sheke wani makiyayi Shuaibu Mati a Rugan Fulani da Samaila Mai Yankan Katako a Tudun Wazata

Kaduna - Miyagun 'yan bindiga da suka kai farmaki jihar Kaduna sun halaka makiyayi a jihar ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kamar yadda rahotannin tsaro suka bayyana, 'yan bindigan sun kutsa Rugan Mati da ke karamar hukumar Giwa ta jihar inda suka sheke wani Shuaibu Mati.

Makiyayi da shugaban Fulani sun sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kai farmaki Kaduna
Makiyayi da shugaban Fulani sun sheka lahira bayan 'yan bindiga sun kai farmaki Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An gano cewa, 'yan bindigan sun sake kutsawa Tudun Amada Wazata da ke Kadage inda suka sheke wani Samaila Mai Yankan Katako har cikin gidansa.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe

Har ila yau, a wani harin da miyagun suka kai, sun halaka shugaban Fulanin yankin mai suna Alhaji Abubakar Abdullahi a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, miyagun sun sace marigayin daga gidansa a sa'o'in farko na ranar Juma'a kuma sun bukaci kudin fansa wanda ya ce bashi da su.

Daga nan suka jagorancesa zuwa kan babbar hanya inda suka bindige shi.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar mummunan lamarin a wata takarda da ya fitar a daren Juma'a.

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna tsananin damuwarsa kan kashe-kashen nan tare da mika ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su.

Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

A wani labari na daban, Laftanal Janar Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa, ya ce duk wani farmaki da aka kai bariki, babu shakka kwamandan barikin zai kama da laifi. Ya sanar da hakan ne yayin rufe taron shugaban sojin kasa da aka yi, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban sojin kasan ya yi kira ga kwamandoji da su tabbatar da cewa sun kasance a shirye kuma suna sa ido a kowanne lokaci domin guje wa farmakin ba-zata.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da cewa, halin baya-baya a bangaren wasu kwamandoji abu ne da ba zai lamunta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng