Da Dumi-Duminsa: Yan Bindiga Sun Hallaka Lauya Har Lahira
- Mutane sun shiga tashin hankali yayin da wasu miyagun yan bindiga suka kutsa kasuwar Supermarket suka bindige lauya
- Rahotanni sun bayyana cewa lauyan na kokarin kare wasu mutane da aka cafke da zargin hannu a tada yamutsi, amma basu da laifin komai
- Kwamishinan yan sandan jihar Imo, Rabiu Hussaini, ya bada umarnin tsananta bincike kan kisan lauyan
Imo - An shiga tashin hankali a jihar Imo, yayin da wasu yan bindiga suka hallaka lauya Darlington Odume, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Odume, wanda aka fi sani da Omokagu, an harbe shi ne a kasuwar supermarket dake Amaifeke, ƙaramar hukumar Orlu a jihar Imo.
Kisan lauyan ya zo ne awanni 24 kacal bayan wasu yan ta'adda sun sheke fadan cocin Anglican, Emeka Merenu, a ƙaramar hukumar Orsu.
Lauya Odume, ɗan asalin ƙauyen Umudara, ya zama cikakken lauya ne ƙarƙashin kungiyar Lauyoyi shekaru 5 da suka shuɗe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa suka kashe lauyan?
Rahotanni sun bayyana cewa lauyan da aka kashe yana kan jagorantar shari'ar wasu mutane da aka cafke da hannu a rikice-rikicen da suka addabi yankin Orlu.
Wata majiya ya bayyana cewa an yi gaggawar kai lauyan asibiti, amma suka ce abin yafi karfinsu a nufi asibitin koyarwa na jami'ar jihar Imo, ya mutu a kan hanyar zuwa asibitin.
Mutumin yace:
"Maharan sun kutsa cikin kasuwar Supermarket ɗin dake Umudara Amaifeke, karamar hukumar Orlu, inda suka harbe shi a ƙirji, suka tsere."
"An yi gaggawar kai shi asibitin dake kusa amma suka ƙi amsar shi, suka umarci a kai shi asibitin koyarwa na jami'ar jihar Imo, amma ya mutu a kan hanya."
"Omekagu yana kokari kan wasu mutane da aka kama waɗanda ake tsammanin basu da laifi kan rikici a Orlu. Matarsa jami'ar yan sanda ce."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Michael Abattam, ya tabbatar da kisan lauyan, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Ya kuma kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar, Rabi'u Hussaini, ya bada umarnin tsananta bincike kan lamarin.
A wani labarin kuma Gwamna Umahi yace sam ba zai baiwa kowa hakuri ba kan kalaman da ya yiwa shugaba Buhari
Gwamnan ya kuma bayyana jin daɗinsa bisa ziyarar Ali Modu Sherif, wanda ke neman tikitin zama shugaban APC na ƙasa.
Umahi yace Shugaba Buhari, shi ne jagora kuma yana da damar zaɓar wanda zai shugabanci APC na gaba.
Asali: Legit.ng