Wajibi Yan Najeriya Su Taimaki FG Wajen Yaki da Matsalar Tsaro a Najeriya, Sanata Lawan
- Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci yan Najeriya kada su zuba ido su bar gwamnatin tarayya da magance matsalar tsaro ita kaɗai
- Sanatan yace tarihi ya nuna yadda shugabannin baya suke haɗa kansu daga kowane yanki domin magance ƙalubalen da ya taso
- Shugaban rundunar sojin ƙasa, Farouk Yahaya, ya bukaci haɗin kai da taimakon yan Najeriya domin dawo da zaman Lafiya a ƙasa
Ekiti - Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmaɗ Lawan, ya yi kira ga yan Najeriya kada su bar gwamnatin tarayya kaɗai wajen yaƙi da matsalar tsaro, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Da yake jawabi a Iyin-Ekiti, jihar Ekiti, Lawan ya bukaci yan Najeriya su ɗauki matsalar da muhimmanci kuma su ɗauka kowa na da rawar da zai iya takawa.
A cewar hukumar dillancin labarai, NAN, sanata Lawan ya ziyarci Iyin-Ekiti ne bisa sarautar da basaraken Iyin-Ekiti, Adeniyi Ajakaye, ya ba shi.
Lawan yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Shugabannin mu da suka kafa Najeriya sun fito daga yankuna daban-daban kuma daga addinai daban-daban, amma suna da manufa ɗaya ta cigaban Najeriya."
"Sun fuskanci ƙalubale sosai, amma sun magance su.Yanzun wasu shugabanni sun zo da kudirin gyara ƙasa da kawo cigaba. Yanzun muna fama da wasu matsalolin kamar na shugbannin baya."
"Yanzun matsalar tsaro ce tafi damun mu a faɗin kasar nan.Wajibi yan siyasa, addinai da kuma sarakunan gargajiya su haɗa kansu wuri ɗaya."
Ta ya hakan zai magance matsalar tsaro?
Sanata lawan ya kara da cewa ko a wane yanki waɗannan matsalolin suke ya kamata mu haɗa karfi da karfe wajen magance su.
"Bai kamata a bar gwamnati kaɗai ta dakile matsalar ba, abu ne na gaggawa, ya kamata mu haɗa kanmu wuri ɗaya mu kawo karshen matsalolin da suka dame mu domin cigaban ƙasa."
2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu
COAS Yahaya ya nemi haɗin kai
Shugaban rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya bukaci haɗin kan yan Najeriya wajen magance matsalar tsaro.
Yace rundunar sojin ƙasa tana aiki ba dare ba rana domin ceto Najeriya daga miyagun ayyukan yan bindiga da sauran yan ta'adda.
Vanguard ta rahoto Yahaya yace:
"Hukumomin tsaro suna kokari sosai wajen ceto Najeriya kuma zamu cigaba da haka domin kawo zaman Lafiya a Najeriya, daga halin da take ciki a yanzu"
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP
Tsohon kakakin shugaban ƙasan da ya gabata, Doyin Okupe, ya gargaɗi jam'iyyar PDP kada ta kai tikitin shugaban ƙasa arewa.
Jigon babban jam'iyyar hamayya ta ƙasa yace jam'iyyar ka iya rasa damarta na kwace mulki daga hannun APC matukar ta yi haka.
Asali: Legit.ng