Labari Mai Dadi: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara biyan ma'aikatan N-Power haƙƙoƙinsu da ta rike a baya
  • Sakataren dindindin na ma'aikatar jin ƙai da walwala, Bashir Alkali, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar
  • Yace ma'aikatan sun fara ganin saƙon shigar kuɗi a asusun bankin su na watanni biyar (N150,000)

Abuja - Ma'aikar jin kai da walwala ta bayyana cewa ta fara biyan ma'ikatan N-Power na rukunin A da B, basukan da suke binta, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren dindindin na ma'aikatar, Bashir Alkali, ya fitar ranar Jumu'a a babban birnin tarayya Abuja.

Alƙali ya bayyana cewa tsarin biyan albashi na gwamnatin tarayya ya dakatar da asusun ma'aikatan N-Power 14,021 a shekarar 2020 bisa wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Wajibi Yan Najeriya Su Taimaki FG Wajen Yaki da Matsalar Tsaro a Najeriya, Sanata Lawan

Ma'aikatan N-Power
Labari Mai Dadi: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar sakataren, daga cikin dalilin da suka haifar da haka sun haɗa da, ma'aikatan na amfani da asusu kala daban-daban wajen karɓar albashi da alawus daga ma'aikatun gwamnatin tarayya fiye da ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren yace yin hakan ya sabawa dokokin shirin N-Power kuma za'a iya kama mutun da zargin aikata cin hanci da rashawa.

Bayan gano haka, wane mataki FG ta ɗauka?

Bugu da ƙari Alkali yace ma'aikatar ta gudanar da bincike tare da haɗin guiwar ma'aikatun gwamnati kuma zuwa yanzun an gano ma'aikata 9,066 da suka dace a biya su kuɗaɗensu.

"Bisa abinda muka gano, albashin waɗannan ma'aikatan N-Power da yakai N150,000 kowannen su ana cigaba da biyansu. Sun fara samun sakon karta kwana na shigar kuɗinsu cikin asusun su yau."
"Za'a cigaba da rike kuɗaɗen sauran mutum 4,955 har sai an kammala gudanar da bincike nan gaba."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

A wani labarin kuma Gwamnonin PDP Sun Maida Martani Kan Ikirarin Gwamnan da Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Kungiyar gwamnonin PDP, (PDP-GF), tace gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ci amanarsu a zaɓen 2019.

Gwamnonin sun faɗi haka ne yayin martani kan tsoma bakin Umahi a abinda ya shafe su da jam'iyyar hamayya PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262