Gwamnonin PDP Sun Maida Martani Kan Ikirarin Gwamnan da Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Gwamnonin PDP Sun Maida Martani Kan Ikirarin Gwamnan da Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

  • Kungiyar gwamnonin PDP, (PDP-GF), tace gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ci amanarsu a zaɓen 2019
  • Gwamnonin sun faɗi haka ne yayin martani kan tsoma bakin Umahi a abinda ya shafe su da jam'iyyar hamayya PDP
  • A cewarsu, PDP ta gama shiryawa domin kwace mulki daga hannun APC da kuma ceto Najeriya

Abuja - Ƙungiyar gwamnonin PDP (PDP-GF), ta zargi gwamnan Ebonyi, David Umahi, da yi wa PDP zagon ƙasa a babban zaɓen 2019, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnan Umahi, wanda ya fice daga PDP, ya koma APC a shekarar 2020, ya yi tsokaci kan rikicin yankin da jam'iyyar adawa zata kai tikitin shugaban ƙasa a 2023.

Umahi yace duk da matsayar gwamnonin kudu na cewa wajibi a kai shugabancin ƙasa yankinsu, amma wasu gwamnonin PDP ba su amince da haka ba.

Kara karanta wannan

Karya Fani-Kayode ya sharara, babu hannunsa a sauya-sheka ta daga PDP inji Gwamnan APC

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi
Gwamnonin PDP Sun Maida Martani Kan Ikirarin Gwamnan da Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Martanin PDP ga gwamna Umahi

Da yake martani kan ikirarin gwamnan, daraktan kungiyar gwamnoni, C.I.D Maduabum, ya shawarci Umahi ya fuskanci abinda ke gabansa a APC, ya kyaƙe PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa yace:

"Muna shawartar gwamna Umahi ya maida hankali kan damuwarsu dake cikin APC kuma ya daina saka PDP da gwamnoninta a cikin abinda bai shafe su ba."
"Jam'iyyar PDP ba ta dogara da kowa ba, tana da tsarinta na gudanar da aiki kuma ta na da dabarun fuskantar komai, ba ta bukatar tallafin APC ko wata ƙumgiya."

Wane yanki PDP zata kai takarar shugaban ƙasa?

Maduabum ya kara da cewa PDP zata yanke hukunci kan rarraba mukamai zuwa yankuna a lokacin da ya dace.

"Ita kanta APC ba ta yanke hukunci ba har yanzun, ƙungiyoyi daban-daban na cigaba da kace-nace kan lamarin don kare wanda suke so, amma daga ƙarshe jam'iyya ce zata ɗauki mataki."

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar Adawa PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Meyasa Gwamna Umahi ya fice daga PDP?

A cewar daraktan ƙungiyar gwamnonin, Umahi ya fice daga PDP zuwa APC ne saboda ƙaunar da yake wa Buhari, da kuma wasu dalilansa.

Yace:

"Gwamna Umahi ya yaudari PDP a zaɓen 2019, abu ne mai kyau da ya koma APC, maimakon ya cigaba da zama yana mana zagon ƙasa a cikin PDP."

Maduabum yace rubutaccen abu ne PDP zata kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC a 2023 domin ceto Najeriya da demokaraɗiyya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma matasan da yan sanda suka cafke, sun faɗi dalilin da yasa suka kashe ɗan sanatan APC a Kaduna

Bashir Muhammad, da Nasiru Salisu, sun ce satar motar mamacin suka je yi gidan kuma sun yi rigima da shi, daga baya suka ɗaure shi.

Kakakin yan sandan Kaduna, Muhammad Jalige, yace ana cigaba da bincike, kuma za'a gurfanar da su gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262