Kudi kimanin N350m sun yi batan dabo daga baitul malin kotun Shari'a a Kano

Kudi kimanin N350m sun yi batan dabo daga baitul malin kotun Shari'a a Kano

  • A gidan adalci, an yi awon gaba da kimanin N350m a jihar Kano
  • An kai karar wannan lamari wajen hukumar yaki da rashawa
  • Shugaban kotunan Shari'a yace kudaden gado ne da aka kai kotu don rabawa

Kano - Kudi Sama da N345million sun yi batan dabo daga asusun babbar kotun Shari'a a jihar Kano, a cewar rahoton gidan rediyon Freedom.

Babban Alkalin kotun Shari'ar jihar Grand Khadi Tijjani Yakasa ya tabbatar da hakan inda yace an kai karan lamarin ofishin sauraron kararraki da yaki da rashawa na Kano domin bincike.

Sakataran kotun, Haruna Khalil, ya bayyana cewa tuni an kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin.

A cewarsa, kudin da suka bata kudaden gadon mutane ne da aka ajiye a hannun kotun domin rabawa masu hakki.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Yace an gano kudaden sun yi batan dabo ne yayinda akayi kokarin cire wasu kudade, kawai sai aka ga milyan 9 kawai suka rage a asusun.

Kudi kimanin N350m sun yi batan dabo daga baitul malin kotun Shari'a a Kano
Kudi kimanin N350m sun yi batan dabo daga baitul malin kotun Shari'a a Kano
Asali: Facebook

An sace kwamfutoci don tsegumi ga bincike

An tattaro cewa bayan nada kwamitin bincike, an sake sace wasu kwamfutoci daga kotun don kawo cikas ga bincke.

A cewar shugaban hukumar yaki da rashawa a hukumar Kano, Mahmud Balarabe, yace an gayyaci dukkan wadanda suke da hannu, ciki har da ma'aikatan banki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel