Farfesan jami'ar Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce yayin sallar Juma'a

Farfesan jami'ar Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce yayin sallar Juma'a

  • Farfesa a wata jami'a ya rasu yayin da yake sallar juma'a jihar Oyo bayan ya yanki jiki ya fadi
  • Rahotanni sun bayyana cewa, farfesan babban ne fannin ilimin kimiyya a duniyar ilimin kimiyya
  • Hukumar jami'ar da yake aiki sun tabbatar da mutuwarsa, hakazalika an bayyana ranar jana'izarsa

Oyo - Wani Farfesa a Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, Ogbomoso, Abass Olajire, ya yanki jiki ya fadi ya mutu ranar Juma’a 17 ga watan Satumba, 2021.

Ya mutu yana dan shekara 59 a duniya.

Wasu majiyoyi a jami'ar sun tabbatar wa jaridar Punch cewa farfesan ya mutu yayin da yake sallar Juma'a a ranar Juma'a.

Majiyoyin dangi sun ce za a binne marigayin a garin Ibadan ranar Asabar mai zuwa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC

Farfesan jami'ar Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce yayin sallar Juma'a
Marigayi Abass Olajire | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Olajire kwanan ya fito cikin jerin manyan malamai a duniya, bisa ga wani matsayi da Elsevier B. V (Netherlands) da kungiyar masu bincike karkashin jagorancin Farfesa John P.A. loannidis daga Jami'ar Stanford ta kasar Amurka.

An ba shi matsayi na 128 cikin 66,925 na manyan masana kimiyyar duniya a cikin watan Maris din bana.

Jami’in hulda da jama’a na LAUTECH, Lekan Fadeyi, shi ma ya tabbatar wa da rasuwar farfesan.

A cewarsa:

"Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami'ar LAUTECH, Farfesa Mojeed Olaide Liasu, wanda ya kadu da samun labarin abin bakin cikin, ya ce Farfesa Abass tauraro ne mai haske a cikin cibiyar kuma ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma bashi gidan aljanna.

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube.

Bawa ya tsaya da magana ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa:

"Don Allah, ku gafarce ni, ba zan iya ci gaba ba."

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Pantami, da wasu manyan mutane sun rike shi, bayan wani lokaci, aka yi masa jagora ya fita daga zauren taron.

A cewar rahoton Daily Trust Jagoran Bikin (MC) daga baya ya ba da sanarwar cewa yanayin Bawa ya dan warware.

A cewarsa:

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Shugaban EFCC a yanzu ya warware."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Ahmad Tage rasuwa

Amma shugaban da wadanda suka hanzarta fitar da shi har yanzu basu komo cikin zauren ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Yadda wani mutum ya dirka wa direban keke-napep duka nan take ya mutu

A wani labarin, an zargi wani direban keke-napep mai suna Kola Adeyemi da laifin dukan wani dan uwansa mai keke-napep a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Daily Trust ta tattaro cewa wanda ake zargin, Kayode Oluwatomi, wanda aka fi sani da “lawyer” ma’aikaci ne na kamfanin tuntuba na BYC da ke yankin Irewolede a Ilorin.

An ce ya farma mamacin ne saboda ya bugi abin hawansa ta baya. Tribune Nigeria ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin 14 ga watan Satumba da misalin karfe 4:30 na yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel