Tattalin Arzikin Najeriya Ba Zai Samu Cigaba Ba Idan Ba Mu Ciyo Bashi Ba, Gwamnatin Tarayya

Tattalin Arzikin Najeriya Ba Zai Samu Cigaba Ba Idan Ba Mu Ciyo Bashi Ba, Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa cigaban tattalin arzikin da aka samu zai samu koma baya idan ba'a ciyo bashi ba
  • Gwamnatin tace idan ta karbo rance tana zuba su ne a ɓangaren gina muhimman ayyuka dake samar da aikin yi
  • Ministan kuɗi, Zainab Ahmed, tace yan Najeriya zasu ɗanɗani romon cigaban da ake samu nan gaba

Abuja - Ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, tace cigaban tattalin arziki na kashi 5.01% da aka samu a rukunin shekara na biyu, 2021 zai samu koma baya idan ba'a ciyo bashi ba.

Ministan tace bashin da gwamnati ke ciyo wa tana zuba shi ne a ɓangaren gina muhimmman ayyukan kasa dake samar da aikin yi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ministan Buhari Ya Fallasa Yadda Ake Sata Ta Karkashin Kasa a Mulkin Shugaba Buhari

Shugaba Buhari da ministan kuɗi, Zainab Ahmed
Tattalin Arzikin Najeriya Ba Zai Samu Cigaba Ba Idan Ba Mu Ciyo Bashi Ba, Gwamnatin Tarayya Hoto: politicsnigeria.com
Asali: UGC

Da take jawabi a Abuja ranar Litinin, a wani taron manema labarai tare da ministan yaɗa labaru, Ali Muhammed, da wasu kusoshin gwamnati, Zainab tace:

"Gwamnatin tarayya tana farin cikin yadda tattalin arziki da harkokin kasuwanci suka fara komawa kamar da tun bayan ɓarkewar korona."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nan gaba yan Najeriya zasu ji daɗi

Ministan ta kara da cewa yan Najeriya ba zasu fahimci amfanin cigaban da ake samu a tattalin arziki ba har sai an wayi gari ya keta yawansu, kamar yadda the nation ta ruwaito

Zainab Ahmed tace:

"Matakin da Najeriya take ciki a yanzun wajen ciyo bashi bai wuce kashi 23% na tattalin arzikin ta ba."
"Na faɗa lokuta da dama cewa babban matsalar Najeriya a yanzun shine hanyar tattara haraji."
"Muna sane da bashin da muke ciyo wa kuma muna karbo su ne domin zuba su a muhimman ayyukan cigaban kasa."

Kara karanta wannan

Idan Bamu Yi Dagaske Ba Wataran Abujan da Muke Takama Ba Zata Zaunu Ba, Ministan Buhari

Ministan ta bayyana cewa a shekarar da ta gabata 2020, an fitar da baki ɗaya tiriliyan N2.4tr na kasafin manyan ayyukan ƙasa, yayin da zuwa yanzun an fitar da tiriliyan N1.4tr daga kasafin bana 2021.

A wani labarin na daban kuma Jami'ai Sun Cafke Wani Bawan Allah da Ya Ɗirkawa Ɗiyarsa Ciki Har Ta Haihu

Yan bijilanti sun damke wani mutumi da ake zargin ya kwanta da ɗiyarsa har ta samu juna biyu kuma ta haife shi a Delta.

Mutumin mai suna Akpokpokpo, ya amsa laifinsa amma yace sau ɗaya ya taba kwanciya da yarinyar kuma giya ya sha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel