Sojoji da Dama Sun Mutu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Yiwa Tawagar Sojojin Kwantan Bauna a Borno

Sojoji da Dama Sun Mutu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Yiwa Tawagar Sojojin Kwantan Bauna a Borno

  • Rahoton dake fitowa daga jihar Borno, ya nuna cewa mayakan Boko Haram sun yiwa jerin gwanon sojoji kwantan bauna
  • Aƙalla dakarun soji 10 suka mutu yayin da yan ta'addan suka mamayi sojoji a kan hanyar zuwa Maiduguri daga Monguno
  • Harin yazo makonni kalilan bayan ɗaruruwan mayakan Boko Haram sun mika wuya ga rundunar sojoji

Borno - Akalla sojoji 10 ne suka kwanta dama yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka wa jerin gwanon sojojin kwantan Bauna a Borno, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin suna kan hanyarsu daga Monguno zuwa Maiduguri yayin da yan ta'addan suka far musu.

Wata majiya ta shaidawa The Cable cewa Sojojin sun fito ne daga ɗaya daga cikin sansanin su dake yankin, kuma suna aikin jigilar kayayyakin su ne zuwa Maiduguri.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Kutsa Supermarket Suka Harbe Wani Lauya Har Lahira

Boko Haram ta yiwa sojoji kwantan bauna
Sojoji da Dama Sun Mutu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Yiwa Tawagar Sojojin Kwantan Bauna a Borno Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Majiyar tace:

"Da alama yan ta'addan sun shirya harin ne tun cikin dare, bayan sun samu bayanai cewa sojoji zasu wuce ta hanyar da safe."
"Akalla sojoji 10 suka mutu, cikinsu harda wani da ake tsammanin kwamanda ne. Waɗanda suka samu raunuka kuma an kwashe su zuwa Asibiti."

Yan ta'adda sun kwashi makaman sojoji

Hakazalika, an tattaro cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da wasu makamai da kayan aikin dakarun sojojin.

Ba'a samu kakakin rundunar sojojin ƙasa, Onyema Nwachukwu, ba domin jin abinda zai faɗa game da harin.

Mayakan Boko Haram sun mika wuya

Wannan harin yazo ne makonni kaɗan bayan ɗaruruwan yan ta'addan sun mika wuya tare da aje makamansu ga rundunar soji.

Legit.ng Hausa ta gano cewa a farkon watan Agusta, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin yan Boko Haram ya mika wuya, tare da neman yan Najeriya su yafe musu.

Kara karanta wannan

Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara

A wani labarin kuma waɗanda yan sanda suka cafke da hannu a kisan ɗan sanatan APC, sun bayyana dalilin shiga gidansa

Bashir Muhammad, da Nasiru Salisu, sun ce satar motar mamacin suka je yi gidan kuma sun yi rigima da shi, daga baya suka ɗaure shi.

Kakakin yan sandan Kaduna, Muhammad Jalige, yace ana cigaba da bincike, kuma za'a gurfanar da su gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel