Tuna baya: A 2019, FFK ya ce gara ya sheka lahira da ya koma APC
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani- Kayode ya taba ikirarin cewa da ya koma APC gara ya sheka lahira
- A wasu wallafa da yayi a Twitter, tsohon ministan ya ce ya shirya sukar jam'iyyar APC da mulkin ta har karshen rayuwarsa
- A yau kwatsam, dan siyasan ya garzaya fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya koma jam'iyyar APC tare da shaidar wasu gwamnoni
Aso Rock, Abuja - Femi Fani Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya sauya sheka inda ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya karbe sa zuwa jam'iyyar mai mulki a karamin taro da aka yi a fadar Aso Rock da ke Abuja a ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.
Wasu gwamnonin jam'iyyar mai mulki sun shaida komen Fani-Kayode zuwa jam'iyyar APC wacce ya bari tun a 2014, lamarin da ya alakanta da banbance-banbance wadanda ba a iya magancewa.
Bayan barin jam'iyyar mai mulki, Fani-Kayode ya dinga caccakar jam'iyyar mai mulki tare da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa hakan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A shekaru biyu da suka gabata, an samu rahotannin cewa ya koma jam'iyyar mai mulki, lamarin da Fani-Kayode ya ce da faruwarsa gara ya sheka lahira.
"Na mayar da hankali wurin sukar jam'iyyar APC da wasu masu manyan mukami na jam'iyyar har karshen rayuwa ta kuma ba zan taba komawa jam'iyyar ba komai zai faru!" ya ce a wancan lokacin.
Ga wasu daga cikin wallafar da tsohon ministan sufurin jiragen saman yayi a Twitter a ranar 15 ga watan Disamban 2019
Babu wasikar jan kunne da 'yan bindiga suka aiko mana, FGC Sokoto
A wani labari na daban, hukumar makarantar FGC Sokoto ta musanta labarin da ya yi ta yawo a kan ta rufe makarantar ne saboda matsalar tsaro.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce shugaban hukumar makarantar, Ibrahim Uba ya sa hannu, ya ce babu batun wata barazana da aka yi wa makarantar.
“In fayyace muku bayani, a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, kungiyar daliban FGC Birnin Yauri 13 aka maido makarantar saboda wani mummunan lamari da ya auku a makarantar a wasu watannin da suka gabata."
Asali: Legit.ng