Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya - EFCC

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya - EFCC

  • Hukumar EFCC ta yi karin haske kan halin lafiyar shugabanta, Abdulrasheed Bawa, wanda ya yanke jiki ya fadi a fadar Shugaban kasa
  • Hukumar a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, ta bayyana cewa a yanzu Bawa yana cikin koshin lafiya
  • EFCC ta ce Shugaban nata ya yanke jiki ya fadi ne a wajen taron sakamakon zazzabin da yaji ya taso masa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi martani a kan yanke jiki da shugabanta yayi a yayin wani taro a fadar Shugaban a ranar Laraba, 16 ga watan Satumba.

A cewar hukumar da ke hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, shugabanta yana nan cikin koshin lafiya.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya - EFCC
Hukumar EFCC ta ce shugabanta, Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, hukumar yaki da cin hanci da rashawar tace akwai bukatar tayi karin haske a kan lamarin duba ga abun da ya faru a fadar Shugaban kasan yayin da Bawa ke jawabin fatan alkhairi.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Shugaban na EFCC dai ya ji zazzabi ya taso masa lamarin da yasa dole ya koma kujerarsa ya zauna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai hukumar ta kara da cewa tuni Shugaban nata ya koma kan kafafunsa bayan ya samu kulawar likita.

Ta ce:

“Shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya.
“Wannan karin haske ya zama dole bayan wani abin da ya faru a yau 16 ga Satumba, 2021 a Fadar Shugaban Kasa, Abuja inda yake ba da sakon fatan alheri ga bikin Ranar Shaida ta Kasa, ya ji rashin lafiya kuma hakan yasa dole ya koma kan kujerarsa.
“Tuni ya sami kulawar likita kuma ya dawo kan teburinsa.”

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Kara karanta wannan

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa.

Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube.

Bawa ya tsaya da magana ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa:

"Don Allah, ku gafarce ni, ba zan iya ci gaba ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel