IPOB: Gwamna Obiano ya bar gidan gwamnati, ya jagoranci zanga-zanga a kan titi

IPOB: Gwamna Obiano ya bar gidan gwamnati, ya jagoranci zanga-zanga a kan titi

  • Willie Obiano da Kwamishinoninsa sun fita zanga-zanga a titunan Awka
  • Gwamnan ya yi kira ga ‘yan kasuwa duk su fita aiki, su bude shagunansu
  • Hakan ya taimaka wajen watsi da umarnin kullen da IPOB tayi wa jama’a

Anambra - A ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya jagoranci zanga-zanga a kan abubuwan da IPOB suke yi.

Willie Obiano ya shirya gagurumar zanga-zanga ne a dalilin umarnin zaman-gidan da kungiyar IPOB mai fafutukar neman kasar Biyafara take bada wa.

A jiya ne Mai girma Willie Obiano ya rika yawo a titunan garin Awka domin mutane su koma bakin kasuwancinsu, su daina zaman-gida a duk Litinin.

Daily Trust tace gwamnan ya dauki Kwamishinoninsa sun ziyarci wasu bankuna da kasuwanni.

Da ya shiga kasuwar Eke Awka da ke babban birnin jihar Anambra, gwamna Obiano ya yi kira ga ‘yan kasuwa su daina biye wa IPOB, su bude shagunansu.

Gwamna Obiano
Gov. Willie Obiano Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

“Dole mu yi kokarin hana wasu tanbadaddu karbe iko da kasarmu. Na zabi in jagoranci wannan domin kawo karshen wannan cin kashi, wulakanci da barazana.”

A sakamakon tattakin da gwamnan da mukarrabansa suka yi, mutane sun fara fito wa neman kudi; an ga bankuna da motocin haya da kasuwanni suna aiki.

A ranar Lahadi ne gwamnan ya yi barazanar rufe bankuna, tashoshin mota da kasuwannin da suka ki fitowa aiki a jiya ranar Litinin saboda barazanar IPOB.

“Ina kira ga matafiya su bi hanyoyinmu a ranar Litinin, ko suna kan mota ko babur ko keke.”
“Idan ba a bude kasuwanni ba, zan tsige shugabannin kasuwan. Idan shugabannin kasuwanni da tashohi ba su bi umarni ba, zan canza su nan da mako biyu.”

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto, Gwamnan yace rufe wuraren aiki da neman kudi da ake yi yana da tasiri ga tattalin arzikin jihar da aka sani da kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel