Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa

Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa

  • Wata kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, ta umarci malami da ya datse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa
  • Kamar yadda lauyan daliba Zainab ya sanar, soyayya ce ke tsakanin Malam Yusuf da ita, kuma ya lakada mata duka saboda ya gan ta da saurayi
  • Alkali Murtala Nasir ya umarci Malam Yusuf da ya biya Zainab kudi har N8, 500 na kudin kara da ta shigar da kuma kudin maganin da ta kashe

Kaduna - Wata kotun shari'a da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Laraba ta umarci wani malamin makaranta, Yusuf Yusuf da ya datse dukkan wata soyayya da ke tsakaninsa da dalibarsa mai suna Zainab Muhammad.

Alkali Murtala Nasir, ya umarci malamin da ya biya N8, 500 ga Zainab a matsayin kudin shigar da kara da kuma kudin asibiti da ta biya bayan mugun dukan da yayi mata.

Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa
Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

Alkalin ya yanke wannan hukuncin bayan sasancin da su biyun suka yi ba a kotu ba, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Tun farko, lauyan mai kara, Ibrahim Shuaibu, ya sanar da kotun cewa, Zainab ta kai rahoton yadda malamin ta ya lakada mata mugun duka gaban 'yan sandan Sabon Gari a ranar 5 ga watan Satumba.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, ya ce Yusuf ya ji mata rauni a fuska da jiki bayan dukan da yayi mata bayan ya ganta tsaye da wani saurayi.

Bayan bincike, lauyan mai kara ya ce malamin ya kasance masoyi ga Zainab Muhammad tun farko.

Laifin ya ci karo da tanadin sashi na 216 da 211 na dokokin Sharia Penal Code 2002. Yusuf ya musanta aukuwar lamarin.

Balle gidan gyaran hali a Kogi: An sake yin ram da fursunoni 114, Hukuma

A wani labari na daban, Hukumar kula da gidajen gyaran hali, NCoS ta samu nasarar kamo mutane 114 cikin su 240 da suka tsere daga gidan gyaran halin Kabba a ranar 12 ga watan Satumba. Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin hukumar, Francis Enobore ya tabbatar da hakan a wata takarda ta ranar Talata a Abuja.

‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan gyaran hali na Kabba a jihar Kogi, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Shugaban hukumar NCoS na kasa, Haliru Nababa, ya dade da bayar da umarni a kan a yi gaggawar kamo wadanda suka kubuce kuma yanzu haka ana ta bincike a kan yadda aka yi aka balle gidan gyaran halin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel