Balle gidan gyaran hali a Kogi: An sake yin ram da fursunoni 114, Hukuma

Balle gidan gyaran hali a Kogi: An sake yin ram da fursunoni 114, Hukuma

  • Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, NCoS, ta kara kamo mazauna gidan gyaran hali na Kabba guda 114 cikin su 240 da suka tsere
  • Kakakin hukumar, Francis Enobore, ya tabbatar da hakan a ranar Talata a Abuja inda ya ce suna cikin wadanda aka saki a ranar 12 ga watan Satumba
  • Dama wasu ‘yan bindiga ne suka kai farmaki gidan gyaran halin Kabba na jihar Kogi kuma dama shugaban hukumar ya shawarci duk wadanda suka tsere su koma

Kabba, Kogi - Hukumar kula da gidajen gyaran hali, NCoS ta samu nasarar kamo mutane 114 cikin su 240 da suka tsere daga gidan gyaran halin Kabba a ranar 12 ga watan Satumba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin hukumar, Francis Enobore ya tabbatar da hakan a wata takarda ta ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jami'an tsaro sun kamo fursunoni 108 da suka tsere daga gidan yarin Kogi

Balle gidan gyaran hali a Kogi: An sake yin ram da fursunoni 114, Hukuma
Balle gidan gyaran hali a Kogi: An sake yin ram da fursunoni 114, Hukuma. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan gyaran hali na Kabba a jihar Kogi, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Shugaban hukumar NCoS na kasa, Haliru Nababa, ya dade da bayar da umarni a kan a yi gaggawar kamo wadanda suka kubuce kuma yanzu haka ana ta bincike a kan yadda aka yi aka balle gidan gyaran halin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sakamakon yadda shugaban hukumar kula da gidan yari na kasa ya yi gaggawar sa hannu a lamarin, yanzu haka an kamo wadanda suka tsere daga gidan guda 114.
“Shi da kan shi shugaban ya jagoranci jami’an sa don zuwa har gidan gyaran halin kuma ya umarci a yi gaggawar fara binciko wadanda suka tsere.

Kamar yadda ya ce, shugaban ya nemi taimakon sauran jami’an tsaro ciki har da ‘Yan sa kai wurin nemo duk wasu ‘yan gidan gyaran halin da suka tsere.

Kara karanta wannan

Bidiyon katon din giya 3,600 da Hisbah ta kama an ɓoye cikin buhunan abincin kaji a Kano

Ya shawarce su da su yi gaggawar komawa gidan cikin sa’o’i 24 don gudun a kara kama su kuma a yanke musu hukunci.

Ya kula da yadda babu wani amfanin wasan buyar da suke yi don yanzu haka akwai hotuna da duk wasu bayanai da za su sa a yi gaggawar kama su.

Ya kara tabbatar wa da jama’a cewa za a kula da lafiyarsu da dukiyoyin su, inda yace jami’an tsaro za su tabbatar da sun nemo duk wani bata-gari a maboyar su.

Damfarar daukar aiki: An dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjayen majalisar Nasarawa

A wani labari na daban, Majalisar jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba wanda aka fi sani da PDP-Obi 2 kan zarginsa da ake da daukar aikin bogi na malamai 38 na makarantun sakandare a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya sanar da wannan yayin zaman majalisar a ranar Litinin a Lafia.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Dakatar da Zhekaba ya zo ne bayan majalisar ta tattauna kan rahoton kwamitin ilimi na majalisar kan daukar aikin malamai 366 da wasu 38 na bogi da aka gani wurin jerin biyan kudin albashi na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel