Har Yanzu Magu Jami'in Gwamnati Ne, Yana Kwasan Albashi, Ministan Buhari Ya Fallasa Bayani

Har Yanzu Magu Jami'in Gwamnati Ne, Yana Kwasan Albashi, Ministan Buhari Ya Fallasa Bayani

  • Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, ya fallasa bayanan halin da ake ciki game da lamarin Ibrahim Magu
  • Ministan ya bayyana cewa tsohon mukaddashin shugaban EFCC ɗin yana nan a tsarin ma'aikatan gwamnatin tarayya dake ɗibar albashi
  • Yace a halin yanzun an mika rahoton binciken kwamiti ga shugaban ƙasa, ana jiran ɗaukar mataki na karshe

Abuja - Ministan harkokin rundunar yan sanda, Muhammad Dingyadi, yace Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban EFCC, ya na cikin tsarin albashi na FG, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Ministan ya yi wannan furuci ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta Channels tv, ranar Talata.

Da yake magana kan lamarin Magu, Ministan ya bayyana cewa tun bayan mika rahoton bincike ga shugaban ƙasa, ba'a sake tuntuɓar ma'aikatar ba ko hukumar yan sanda.

Kara karanta wannan

Babu Wani Ministan da Ya Ɗauki Matakan Kakkaɓe Yan Ta'adda A Najeriya Kamar Sheikh Pantami, Kayode

Tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu
Har Yanzu Magu Jami'in Gwamnati Ne, Yana Kwasan Albashi, Ministan Buhari Ya Fallasa Bayani Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Minista Dingyadi yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abinda na sani shine an mika sakamakon bincike ga shugaban ƙasa, kuma har zuwa yanzun ba'a tuntubi ma'aikatar yan sanda ko hukumar yan sanda ba game da lamarin."
"A halin yanzun muna jiran mu ji abinda sakamako na ƙarshe zai fito, a bayyana wa kowa yasani."

Shin har yanzun Ibrahim Magu ma'aikacin gwamnati ne?

Ministan yace duk da an dakatar da Ibrahim Magu, daga muƙamin mukaddashin shugaban EFCC, har yanzun shi jami'in rundunar yan sanda ne kuma yana karkashin tsarin albashi na gwamnatin tarayya, Punch ta ruwaito.

"Kamar yadda kuka sani an gudanar da bincike, kuma mutumin yana nan kan aikinsa, yana nan a hedkwatar yan sanda. Bana son yin magana sosai a wannan lokacin game da abinda ya faru da rahoton kwamiti."
"Har yanzun shi ɗan sanda ne, duk da an dakatar da shi. Amma abinda kowa ya sani ya rike mukamin mukaddashin EFCC, yanzun kuma ya bar wurin."

Kara karanta wannan

Al'ummar Sokoto Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Aike Musu da Wasikar Barazana

"Hakan ba yana nufin ya fita tsarin albashin FG bane, shi ma'aikaci ne, jami'in ɗan sanda ne daga nan har zuwa sanda aka ɗauki mataki na karshe kan lamarin."

Matar Ganduje ta halarci bikin kammala karatun ɗanta a Landan

A wani labarin kuma bayan fatali da gayyatar hukumar EFCC kan wata badaƙala, Matar Ganduje ta shilla birnin Landan

Hukumar EFCC ta gayyace ta ne ranar Alhamis, bayan babban ɗanta, Abdul-azeez ya shigar da korafi a kanta.

Gwamna Ganduje na jihar Kano da sauran mambobin iyalansa sun samu halartar bikin a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262