Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama

Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama

  • Wani jirgin yaki ya kai hari a kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe
  • Lamarin ya yi sanadiyar rasa ran 'yan fararen hula da dama a safiyar ranar Laraba, 15 ga watan Satumba
  • Sai dai rundunar 'yan sandan jihar bata tabbatar da harin ba, tace bata da labarin lamarin

Yobe - Wani rahoton sashin Hausa na BBC ya nuna cewa wani jirgin yaki da ba a tabbatar daga inda yake ba ya yi luguden wuta a kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.

Lamarin wanda ya afku a safiyar yau Laraba, 15 ga watan Satumba, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama.

Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama
Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama
Asali: Original

Kafar yada labaran ta bayyana cewa mazauna yankin sun sanar mata da cewar sun wayi gari ne da ganin jiragen yaki har guda uku suna sintiri a yankin nasu.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

Wani mutum da ya rasa yan uwansa a harin ya shaida wa sashin labaran cewa daga baya sai daya daga cikin jiragen ya yi luguden wuta kan wani bangare na garin.

Ya bayyana cewa jirgin babba ne irin na sojoji amma basu san daga inda ya fito ba.

A cewarsa:

"Da misalin karfe 8.30 na safe ne abin ya afku, har zuwa lokacin da daya daga cikin jiragen ya fado wani bangaren na garin yana ta barin wuta, duk gidajen da ke bangaren sai da suka lalace."

Ya kuma bayyana cewa basu san adadin mutanen da suka mutu ba amma ko a gidansu matar mahaifinsa da 'yar yayarsa sun mutu.

Har ila yau ya ce babu wani jami’in tsaro da ya je wajen "domin da akwai yaran Boko Haram da ke shawagi sosai a yankin."

Kara karanta wannan

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

Idon shaidan ya ce su yan gari ne suka yi aikin kwasar gawarwaki tare da wadanda suka jikkata zuwa asibitn garin Geidam.

Sai dai kuma da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdurrahman, ya bayyana cewa basu da masaniya a kan lamarin, amma ya ce zai tuntubi sashin BBC idan ya samu cikakken bayani.

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta'adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna daga Dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel