Al'ummar Sokoto Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Aike Musu Wasikar Barazana

Al'ummar Sokoto Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Aike Musu Wasikar Barazana

  • Miyagun yan bindiga sun aike da wasikar barazana ga mutanen ƙauyuka biyar a kananan hukumomin Sokoto
  • Lamarin ya jefa mutanen yankunan cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar kan yaushe maharan zasu shigo
  • Wasikar ta bayyana cewa babu wani karfin jami'an tsaro da zai hana su aiwatar da kudirinsu na kawo harin

Sokoto - Yan bindigan da suka gudo daga jihar Zamfara, waɗanda suka kai hari kan kauyukan dake bakin boda a Sokoto makon da ya shuɗe, sun aike da wasikar cigaba da miyagun ayyukansu ga mutanen yankin.

Maharan, waɗanda ake zargin sun tsero ne daga luguden wutan sojoji a Zamfara sun kai hare-hare kananan hukumomi biyu a jihar Sokoto.

Miyagun sun kai hari kananan hukumomin Dange/Shuni da kuma Tureta, ranar Talata da Laraba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

Yan bindiga sum aike da barazana
Al'ummar Sokoto Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Aike Musu Wasikar Barazana Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa harin yan bindigan a waɗannan yankuna ya hallaka mutane da dama yayin da suka fasa shaguna domin ɗibar kayan abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wace barazana yan bindigan suka yi?

Mutanen Kauyen Shuni sun shiga tashin hankali da zaman ɗar-ɗar, biyo bayan tsintar wasikar barazanar mahara da aka yi karkashin wata bishiya.

A cewar wani mazaunin kauyen, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, yace an tsinci wasikar ne a karkashin wata bishiya dake kauyen Kwanar Kimba, karkashin Shuni.

Mutumin yace:

"Takardar wasikar an rubuta ta da harshen Hausa, wanda ake zargin yan bindiga da barzanar tarwatsa kauyukan Shuni, Kwanar Kimba, Rikina da Dange, kuma hakan ya jefa al'umma cikin tashin hankali."

A wasikar sun bayyana cewa babu wani karfin jami'an tsaro da zai hana su aiwatar da mummunan kudirinsu.

"Sojoji miliyan ɗaya ba su isa dakatar da mu kawo muku hare-hare ba, wanda zamu iya yi kowane lokaci daga yanzun."

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Damke Kasurgumin Dan Bindiga da Wasu Yan Leken Asiri da Dama a Katsina

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Har yanzun babu wani sako a hukumance da rundunar yan sanda reshen jihar Sokoto ta fitar game da lamarin, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Amma wata majiya da shaida wa yan jarida cewa har yanzun hedkwatar yan sandan jihar ba ta samu kwafin takardar daga DPO na yankin ba.

A wani labarin kuma SERAP Ta Aike da Budaddiyar Wasika Ga Shugaba Buhari Kan Datse Hanyoyin Sadarwa a Zamfara da Katsina

Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban ƙasa Buhari ya gaggauta dakatar da matakin datse sabis a Zamfara da Katsina.

A cewar kungiyar wannan matakin ya kara wa al'ummar yankin matsin rayuwa banda wanda suke ciki a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel