Bayan Ta Yi Fatali da Gayyatar EFCC, Matar Ganduje Ta Shilla Landan Wurin Bikin Kammala Karatun Ɗanta
- Matar gwamnan jihar Kano, Hafsat Abdullahi Ganduje, ta shilla birnin Landan domin halartar bikin kammala karatun ɗan autanta
- Wannan na zuwa ne bayan Hajiya Hafsat ta yi fatali da katin gayyata da hukumar EFCC ta aike mata
- Gwamna Ganduje na jihar Kano da sauran mambobin iyalansa sun samu halartar bikin a birnin Landan na kasar Birtaniya
Kano - Matar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Ganduje, ta shilla Landan domin halartar bikin kammala karatu na ɗaya daga cikin 'ya'yanta, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Matar gwamnan ta fice daga ƙasar ne bayan ta yi fatali da gayyatar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC kan zarginta da hannu a badaƙalar filaye.
Hukumar EFCC ta gayyace ta ne ranar Alhamis, bayan babban ɗanta, Abdul-azeez ya shigar da korafi a kanta.
Shin su waye suka halarci bikin yaye ɗaliban a Landan?
Mai taimakawa matar gwamnan ta fannin yaɗa labarai, Abubakar Ibrahim, shine ya sanar da tafiya Landan ɗin ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ibrahim yace:
"Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, matar gwamna Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje da sauran iyalai sun halarci bikin kammala karatun karamin ɗansu, Muhammad Abdullahi Ganduje."
"Muhammad ya kammala karatun digirinsa na farko daga jami'ar Regent dake Birnin Landan, ranar 14 ga watan Satumba, 2021."
Wace gayyata EFCC ta yi wa matar Ganduje
Hukumar EFCC ta gayyaci matar gwamnan Kano zuwa hedkwatar ta dake babban birnin tarayya Abuja, domin ta amsa wasu tambayoyi ranar Alhamis.
Babban ɗanta, Abdul-azeez Ganduje, shine ya kai korafin mahaifiyar tasa gaban EFCC, bisa zargin tana amfani da karfin mulki wajen mallakar wasu abubuwa a ƙashin kanta.
Legit.ng Hausa ta gano cewa a baya shi kanshi mai girma gwamnan Kano ya shiga irin waɗannan zargi na sama da faɗi da dukiyar al'umma.
A wani labarin kuma shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya rantsar da sabon sanatan PDP
Sanatan wanda kotun koli ta tabbatar da sahihancin takararsa karkashin PDP, ya fara aiki ne ranar Laraba.
Sanata Agom Jarigbe zai maye gurbin wanda aka rantsar da farko, Steven Odey, daga mazaɓar Cross Rivers ta arewa.
Asali: Legit.ng