Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma

Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma

  • Hasashe sun nuna cewa mutum daya daga cikin Nasiru Baballe Ila, Alhaji Akibu Ibrahim Bello, Ismaeel Buba Ahmed da Suleiman AbdulRahman na iya zama sabon ministan Shugaba Buhari
  • Hakan ya biyo bayan sallamar ministoci biyu na noma da lantarki da shugaban kasar yayi
  • Sai dai kuma babu wani tabbaci a hukumance da ke nuna haka, domin duk shawara ce ta wasu jiga-jigan APC da ke ganin sun cancanta

Abuja - Biyo bayan korar Sabo Nanono daga mukamin ministan aikin gona, wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna mutane hudu da Shugaba Muhammadu Buhari ka iya nadawa don maye gurbinsa.

A cewar rahoton, ana kara samun karin haske kan hasashen wanda ka iya maye gurbin Nanono.

Kara karanta wannan

Nadin Minista: An bayyana Kawu Sumaila da Ahmad a matsayin wadanda ka iya maye gurbin Nanono

Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma
Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Nanono wanda aka kora a ranar Laraba, 1 ga Satumba ya fito ne daga jihar Kano. An tattaro cewa 'yan uwansa sun fara zawarcin gaske don ganin wanda ya maye gurbin ya fito daga jihar.

Ga jerin mutum hudu da ka iya maye gurbin Nanono, a cewar rahoton:

1. Suleiman AbdulRahman (wanda aka fi sani da Kawu Sumaila), tsohon babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan al'amuran majalisar dokoki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Ismaeel Buba Ahmed, Babban Mataimaki na Musamman ga shugaba Buhari kan Shirin tallafawa jama’a na kasa.

3. Nasiru Baballe Ila, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci mazabar Tarauni a majalisar dokokin kasar.

4. Alhaji Akibu Ibrahim Bello, tsohon shugaban karamar hukumar Nassarawa.

Duk da haka Daily Trust ta lura cewa babu wata kungiya a Kano da ta yi kira ga shugaban kasa a hukumance kan ya nada wani daga cikin mutanen da aka lissafa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

An dai jero su ne kawai yayin da wasu jiga -jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulki suka ba da shawarar a matsayin wadanda za su iya maye gurbin.

Shugaba Buhari ya sallami shugaban NAPTIP, Basheer Garba

A wani labari, Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar hana safarar mutane watau NAPTIP, Sanata Basheer Garba Mohammed, daga kujerarsa a ranar Laraba, 8 ga Satumba, 2021.

Buhari ya sallami Basheer ne bayan kimanin watanni hudu da nadashi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana jawabin da ya saki da yammacin nan cewa Buhari ya maye gurbin Sanata Bashir da Fatima Waziri-Azi.

Shehu ya saki jawabin a shafinsa na Facebook. A cewarsa, Buhari ya nada Fatima Waziri-Azi ne bisa shawarar da Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel