Da dumi-dumi: Majalisar dokokin Kano ta ba Ganduje awa 48 ya kori shugaban hukumar haraji ta jihar
- Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi a kori shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar, AbduRazak Salihi
- Majalisar ta bukaci Gwamna Abdullahi Ganduje ya aikata hakan cikin sa'o'i 48
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da rikicin harajin VAT
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta ba da shawarar korar AbduRazak Salihi, shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A zaman majalisar na ranar Talata, 14 ga watan Satumba, ‘yan majalisar sun nemi Gwamna Abdullahi Ganduje ya sauke Salihi cikin sa’o’i 48.
A ranar Litinin, Daily Trust ta ba da rahoton yadda majalisar ta gayyaci Salihi a kan matakin da jihohin Ribas da Legas suka dauka don ci gaba da tattara Harajin kayayyaki (VAT) da kuma sukar da aka yi wa Kano saboda faɗuwa daga cikin jihohi da suka fi tattara kudaden shiga duk da matsayinta na cibiyar kasuwanci ta ƙasar.
Daga matsayinta na biyu bayan Legas, Kano ta faɗi zuwa matsayi na 10 a jerin jihohin da ke samun kuɗin shiga.
Da yake kare shawarar majalisar, Kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya ce halin Shugaban ne ya tursasa su daukar irin wannan matakin.
Ya zargi Sahili da gaza bayyana tarin kudaden shiga na Jiha duk da jerin bukatun majalisar.
Haka kuma, majalisar ta kuma zargi Shugaban na KIRS da hada baki da gwamnati ba tare da saninta ba don rage farashin gidan IPMAN daga N250 zuwa N100, wanda majalisar ta bayyana a matsayin sabawa kundin tsarin mulki.
A jawabansu daban-daban, 'yan majalisar sun amince da "rashin kokarin Shugaban ta fuskar tara kudaden shiga da kuma rashin sanin menene kudaden shiga".
Shugaban majalisar ya ce majalisar ta kafa kwamiti na mutum takwas don binciken hukumar a karkashin Salihi.
Ya lissafa raguwar samun kudaden shiga daga cikin batutuwan da za a bincika.
Kwamitin mutum takwas, wanda Shugaban Kudin Majalisar, Magaji Dahiru Zarewa zai jagoranta, zai gabatar da rahotonsa cikin wata guda.
Akwai yiwuwar albashin ma’aikatan Hukumar FIRS ya ragu a dalilin rikicin VAT da Gwamnoni
A wani labarin, mun ji cewa an samu karin wasu jihohi biyu bayan Legas da Ribas da za su kawo dokar da za ta ba su damar karbar harajin VAT da kansu.
Akwa Ibom da Ogun za su shiga sahun gwamnatocin Ribas da kuma Legas da za su hana jami’an FIRS tattara harajin kayan masarufi a Jihohinsu.
Rahoton yace a daidai wannan lokaci ma’aikatan hukumar FIRS da ke karbar VAT sun tsure a game da wannan mataki da gwamnoni ke dauka.
Asali: Legit.ng