Bayan Kwana 100 da Hana Hawa Twitter, Rahoto Ya Bayyana Biliyoyin Nairorin da Najeriya Ta Yi Asara
- Bayan cikar kwana 100 da hana amfani da Tuwita, Najeriya ta yi asarar biliyoyin kuɗin shiga saboda matakin
- Rahoto ya nuna cewa Najeriya na rasa kimanin miliyan N103.17m a kowace awa ɗaya tun bayan ɗaukar matakin
- A kwanakin bayan ministan yaɗa labarai yace gwamnati ta kusa cimma matsaya da kamfanin Tuwita, kuma zata ɗauke hanin da ta yi
Abuja - Hana hawa dandalin sada zumunta na Tuwita a Najeriya ya shafe kwanaki 100 cif, kuma a tsawon wannan lokacin kasar ta rasa kuɗaɗen shiga kimanin biliyan N247.61bn, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa a ranar 4 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta sanar da hana amfani da tuwita a faɗin kasar Najeriya.
SERAP Ta Aike da Budaddiyar Wasika Ga Shugaba Buhari Kan Datse Hanyoyin Sadarwa a Zamfara da Katsina
Wannan matakin na gwamnati ya zo ne dai-dai lokacin da kamfanin Tuwita ya goge rubutun shugabn ƙasa, Muhammadu Buhari.
Kamfanonin sadarwa sun rufe hawa Tuwita
Bayan matakin FG, kamfanonin sadarwa a ranar 5 ga watan Yuni, sun rufe damar amfani da Tuwita, bayan samun umarnin haka daga hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC).
Bisa wannan lamarin ne, ƙungiyar kamfanonin sadarwa masu lasisin zama a Najeriya (ALTON) ta bayyana cewa:
"Mu ALTON, muna farin cikin sanar da cewa mambobinmu sun samu umarni daga hukumar sadarwa NCC, cewa su dakatar da amfani da shafin Tuwita."
"Ƙungiyar ALTON ta aiwatar da umarnin NCC cikin biyayya kuma ba tare da karya dokokin kasa da kasa ba."
A rahoton NetBlocks, a kowace awa ɗaya Najeriya na rasa miliyan N103.17m kuma yanzun awanni 2,400 da rufe Tuwita.
Yaushe za'a cigaba da amfani da Tuwita?
A kwanakin nan, ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace gwamnati ta kusa cimma yarjejeniya da kamfanin Tuwita, kuma ba da jimawa ba zata ɗage umarnin hanin.
Najeriya ta shiga sahun kasashe irin su China, Korea ta Arewa da Iran, inda aka dakatar da amfani da Tuwita.
A wani labarin kuma Mijin Kasar Italy Ya Harbe Matarsa Yar Najeriya Har Lahira a Gaban Abokan Aikinta, FG Ta Shiga Lamarin
Gwamnatin tarayya ta nemi a yi cikakken bincike kan musabbabin kashe matar aure yar Najeriya, Rita Amenze, a kasar Italiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoto ya nuna cewa mijin ɗan kimanin shekara 61, ya aikata haka ne biyo bayan shigar da bukatar saki da matar ta yi gaban kotu.
Asali: Legit.ng