Bayan shekaru 10 da aure, ya gwabje matarsa mai tsohon ciki saboda abinci, ta sheka barzahu

Bayan shekaru 10 da aure, ya gwabje matarsa mai tsohon ciki saboda abinci, ta sheka barzahu

  • Wani Mutumi ya kama matarsa da duka cikin dare, ya yi sanadiyyar ajalinta
  • Magidancin ya dawo gidansa bayan ya sha giya, ya nemi a kawo masa abinci
  • Matarsa mai ciki tace babu abinci domin ba ayi cefane ba, sai yayi mata duka

Enugu - Wani mummunan lamari ya auku a kauyen Ogwuagor, yankin Abakpa Nike, a Enugu, inda wani mai matsakaitan shekaru ya kashe matarsa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan lamari ya auku ne a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021.

Wannan mutum mai sana’ar karafuna a unguwar Abakpa ya dawo gida bayan ya sha giya, ya yi tatil, sai ya bukaci mai dakinsa ta kawo masa abinci.

Tuwon dare ya jawo an rasa rai

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Rahoton yace wannan Baiwar Allah ba ta ba mijin na ta mai ‘ya ‘ya hudu abinci ba, shi kuma ya ji haushi har ya yi mata ‘dan-karen duka a cikin daren.

Nan-take makwabta suka sheka da ita zuwa asibiti bayan ta fadi. A safiyar ranar Alhamis, likitoci suka tabbatar wa ‘yanuwa cewa wannan matar ta cika.

Marigayiyar wanda aka fi sani da Mama Goodluck a Abakpa tana dauke da tsohon ciki na kusan wata takwas, haihuwa yau ko gobe a lokacin da ta mutu.

Sufetan 'Yan Sanda
Sufetan 'Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Jaridar tace wannan mata ta shafe shekaru sama da goma tana auren mai gidanta a Ogwuagor Abakpa. An saba jin ma’auratan suna fada a tsakaninsu.

Yadda abin ya auku?

Wani mazaunin yankin na Ogwuagor Abakpa, ya shaida manema labarai cewa marigayiyar ta hana shi abinci ne saboda mai gidan bai bar kudin cefane ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Majiyar tace sai dai matar ta nemo garin rogo a makwabta domin ta iya ciyar da ‘ya ‘yansu a ranar.

Mama Goodluck tana hana shi abinci, sai yayi mata duka, har ta kwanta. ‘Yan sa-kai na yankin sun kama magidancin, sun mika shi ga ‘yan sanda a Abakpa.

Dave Umahi ya yi daidai

An samu rahoto cewa Dave Umahi yana nan a kan bakarsa, gwamnan yace bai yi nadamar yi wa Najeriya fatan samun irin Muhammadu Buhari bayan 2023 ba.

Gwamnatin Ebonyi ta kare gwamna Dave Umahi tace suna tare da shugaban kasa Buhari domin Gwamnatin baya ce ta jawo matsalar tsaro da aka gada a 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel