Da Dumi-Dumi: Yan Majlisar Dokoki Sun Dakatar da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye Kan Zargi
- Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta sanar da dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Iliya Zhekaba
- Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bisa rahoton kwamitin ilimi da ya nuna yana da hannu a ɗaukar malamai ba kan ka'ida ba
- Kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya kafa kwamitin wucin gadi na mutum uku da zai binciki lamarin
Nasarawa - Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba (PDP-Obi 2), bisa zarginsa da hannu a ɗaukar malaman sakandire ba bisa ƙa'ida ba a jihar.
Kakakin majalisar dokokin, Ibrahim Abdullahi, shine ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Litinin a Lafia, babban birnin jihar, kamar yadda punch ta ruwaito.
Majalisar ta dakatar da Zhekaba bayan nazari kan rahoton kwamitin ilimi dangane da ɗaukar malamai 366 da kuma wasu 38 da aka gano cikin tsarin biyan albashi, waɗanda aka ɗauka ba bisa ƙa'ida ba.
Majalisa ta kafa kwamitin bincike
Kakakin majalisar ya kafa kwamitin wucin gadi na mutum uku wanda zai gudanar da bincike kan wanda aka dakatar kuma ya kawo rahoto cikin mako biyu, kamar yadda Channesl tv ta ruwaito.
Wani sashin jawabin kakakin majalisar yace:
"Kwamiti ya bukaci a dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Iliya Zhekaba, kuma a kafa kwamitin wucin gadi da zai bincike kan ruwa da tsakin da yayi wajen ɗaukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba."
"A halin yanzun na kafa kwamitin wucin gadi na mutum uku da zasu yi bincike kan hannun wanda ake zargi wajen ɗaukar ma'aikata ta bayan fage, kuma su kawo mana rahoto cikin mako biyu."
"Ba zan iya cewa komai ba kan zargin da ake masa har sai kwamiti ya kammala bincike, yayin da zasu fara bincike, ina wa yan kwamiti fatan nasara."
Su waye mutum uku a kwamitin?
Kakakin majalisar ya bayyana cewa Hon. Suleiman Yakubu Azara, mai wakiltar mazabar Awa ta kudu a matsayin shugaban kwamitin.
Hakanan kuma Hon. Usman Shafa, mai wakiltar mazaɓar Toto/ Gadabuke da kuma Hon. Samuel Tsebe, mai wakiltar Akwanga ta kudu su ne mambobin kwamitin na wucin gadi.
A wani labarin kuma babbar magana, Shahararren Ɗan Kasuwa Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotun Musulunci Kan Jaririn da Ta Haifa
Wani shahararren Ɗan kasuwa mai suna, Abdulhamid Yakubu, ya shigar da tsohuwar matarsa kara a kotun musulunci dake zamanta a Anguwar Magajin Gari, jihar Kaduna.
Mutumin ɗan kimanin shekara 57 a duniya ya yi karar matarsa ne, yana musanta ikirarin cewa jaririn dake hannunta na shi ne.
Asali: Legit.ng