Babbar Magana: Shahararren Ɗan Kasuwa Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotun Musulunci a Kaduna

Babbar Magana: Shahararren Ɗan Kasuwa Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotun Musulunci a Kaduna

  • Wani ɗan kasuwa ya maka tsohuwar matarsa a gaban kotun musulunci, inda ya musanta cewa ba shine uban jaririn da ta haifa ba
  • Tsohuwar matar tasa ta bayyana wa alkalin kotun cewa ɗan da ta haifa bayan mutuwar aurenta na tsohon mijin ne
  • Alkalin kotun, Malam Murtala Nasir, ya umarci kowane ɓangaren ya zo da magabacinsa a zama na gaba

Kaduna - Wani shahararren Ɗan kasuwa mai suna, Abdulhamid Yakubu, ya shigar da tsohuwar matarsa kara a kotun musulunci dake zamanta a Anguwar Magajin Gari, jihar Kaduna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Mutumin ɗan kimanin shekara 57 a duniya ya yi karar matarsa ne, yana musanta ikirarin cewa jaririn dake hannunta na shi ne.

Yakubu ya shaidawa kotu cewa tun kafin ta haifi yaron ya tabbatar mata cikin ba na shi bane, amma har yanzin tana ikirarim cewa jaririnta na tsohon mijin ne.

Kara karanta wannan

Bayan Kwana 100 da Hana Hawa Twitter, Rahoto Ya Bayyana Biliyoyin Nairorin da Najeriya Ta Yi Asara

Dan kasuwa ya shigar da kara Kotu
Babbar Magana: Shahararren Ɗan Kasuwa Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotun Musulunci a Kaduna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ɗan kasuwan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tun kafin na sake ta a watan Maris 2021, na faɗawa yayarta cewa cikin da take ɗauke da shi ba nawa bane domin ta fice daga gidana ba tare da izinina ba."

Matar ta bayyana cewa yaron na tsohon mijin ne

A ɓangarenta, tsohuwar matar Yakubu, ta bayyana cewa ta haifi ɗan ne a watan Agusta 2021, watanni kaɗan bayan rabuwarsu.

Bugu da ƙari matar ta shaidawa alƙalin kotun cewa jaririn da ta haifa bayan rabuwarsu na tsohon mijinta ne.

Kotu ta dage sauraron karar

Bayan sauraron dukkan ɓangarorin biyu, alkalin kotun, Mai shari'a Malam Murtala Nasir, ya umarci ma'auratan su gabatar da waɗanda zasu tsaya musu a zama na gaba.

Daga nan sai alkalin ya bayyana dage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Satumba lokacin da zasu dawo a cigaba da shari'ar.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 da aure, ya gwabje matarsa mai tsohon ciki saboda abinci, ta sheka barzahu

A wani labarin kuma Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna

Ɗiyar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , Zahra Buhari, ta yabawa abokin rayuwarta Ahmad Indimi, cikin soyayya da kauna, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Zahra ta yabawa mijin nata ne kasancewarsa abokin rayuwa nagari na tsawon shekarun da suka shafe tare da juna.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel