Tsohon Shugaban Afghanistan ya nemi afuwar mutanen ƙasar kan tserewar da ya yi Dubai ya bar su hannun Taliban

Tsohon Shugaban Afghanistan ya nemi afuwar mutanen ƙasar kan tserewar da ya yi Dubai ya bar su hannun Taliban

  • Tsohon shugaban kasan Afghanistan, Ashraf Ghani ya bayar da hakuri bisa bai wa hammatar sa iska da ya yi ya tsere Dubai
  • Ya nemi afuwar ne ta shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook inda yace ya tafi ne ba a son ran sa ba
  • Ghani ya musanta zargin da ake ma sa da wawurar kudade masu yawa kafin ya tsere inda yace ko takalmin sa bai samu damar sa wa ba

Dubai - Tsohon shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani ya nemi afuwar mutanen Afghanistan bayan tserewa daular larabawa ya bai wa Taliban mulki a watan da ya gabata, BBC ta ruwaito.

Ghani ya bar Afghanistan ne bayan mayakan Taliban sun kai wa fadar sa farmaki a ranar 15 ga watan Augusta. Rahotanni sun nuna ya tsere Dubai da dala miliyan 169 amma ya musanta wannan zargin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Tsohon Shugaban Afghanistan ya nemi afuwar mutanen ƙasar kan tserewar da ya yi Dubai ya bar su hannun Taliban
Tsohon shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani, ya nemi afuwar al'ummar kasarsa. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Barin Kabul ba karamin al’amari bane a rayuwa ta,” a cewar Ghani a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani.
“Ku yi hakuri ban iya jajircewa na kawo karshen lamarin ta wata hanyar ba”.
A cewar sa bai yi niyyar barin mutanensa a haka ba amma “hakan ce kadai hanyar da zan iya bi”.

A cewar Ghani ba ya da wani tsimi balle dabarar kawo karshen kashe-kashe idan ba barin kasar ya yi ba.

“Na bar kasar bisa roko na da jami’an tsaron fada ta suka yi ne, wadanda suka shawarce ni da in cire kai na daga hatsari saboda fada ne da tun 1990 lokacin yakin farar hula ake yin shi,” kamar yadda ya wallafa, ya kara da cewa ya yi hakan ne don tseratar da Kabul da mutane miliyan 6 ‘yan kasar”.

Kara karanta wannan

‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

A cewarsa ya kwashe shekaru 20 yana kokarin taimakon Afghanistan don ta zama kasar demokradiyya kuma ta samu cigaba.

Ya kara da cewa ya yi da ya sanin barin kasar a halin da take yanzu don haka yara da jikoki za su taso.

A wata wallafar sa ta shafinsa na Facebook ta ranar 18 ga watan Augusta ya ce matsa masa jami’an tsaro sa suka yi saboda akwai alamun za a iya kama shi a hallaka shi.

A cewar sa har fadar sa Taliban suka shiga suna neman sa wuri-wuri.

Ya musanta yadda ake zargin sa da kwasar kudade masu yawan gaske kafin ya bar kasar inda Ghani ya ce 'bai samu damar daukar takalmin sa ya sa ba balle kudade'.

Taliban da sanar da sabon shugaba da sabbin ministoci

A wani labari daban, Kungiyar Taliban ta sanar da Mullah Mohammed Hassan Akhund a matsayin sabon shugaban gwamnatinta a Afghanistan a yau Talata, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da sauran kwana a gaba, bindigar ‘Dan sanda ta kusa kashe Sanata Uba a wajen kamfe

Babban mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid ya shaidawa manema labarai ya sanar da cewa wanda aka kafa Taliban da shi Abdul Ghani Baradar shine zai zama mataimakin shugaban kungiyar.

A cewar kakakin na Taliban sabon ministan harkokin cikin gida shine Sarajuddin Haqqani kamar yadda LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel