'Yan daba sun kai wa 'yan kwana-kwana hari a Kogi, sun raunata wasu sun lalata motar kashe gobara

'Yan daba sun kai wa 'yan kwana-kwana hari a Kogi, sun raunata wasu sun lalata motar kashe gobara

  • ‘Yan daba sun kai wa wasu jami’an hukumar kwana-kwana farmaki a Lokoja, jihar Kogi inda suka ji masa miyagun raunuka
  • Jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranara Juma’a
  • A cewar sa an kira hukumar su don kashe wata gobara ne, suna isa ‘yan daba suka far musu da makamai

Kogi - Wasu ‘yan daba sun kai wa jami’in hukumar kashe gobara farmaki a Lokoja, jihar Kogi, inda suka yi musu kaca-kaca da makamai, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an hukumar, Ugo Huan, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a wacce ya gabatar wa da manema labarai.

'Yan daba sun kai wa 'yan kwana-kwana hari a Kogi, sun raunata wasu sun lalata motar kashe gobara
Jami'an hukumar kashe gobara. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda rikicin Zamfara ya dauko asali shekaru 150 da suka wuce tun kafin zuwan Bature

Yadda lamarin ya faru

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takardar ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba akan titin Felele lokacin da jami’an hukumar kwana-kwanan suka nufi inda gobara ta kama wata mota a gidan man Al-Salam dake kallon Kogi State Polytechnic.

Bayan an kira hukumar an sanar da su cewa gobara ta kama wata mota, isar su ke da wuya suka ga ‘yan daba sun fara kai musu farmaki da makamai.

Sai da suka lalata babbar motar su sannan suka ji wa jami’an hukumar raunuka, yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyar su.

Ba wannan bane karo na farko da hakan ya faru ba.

“Wannan ne karo na biyu a jihar Kogi da ake kai wa jami’an hukumar kwana-kwana farmaki,” kamar yadda takardar tazo.

‘Yan sanda suna bincike akan lamarin.

Daily Trust ta ruwaito yadda Huan da kanshi yace an kai wa ‘yan sanda rahoto kuma suna bincike don kamo duk wadanda suke da hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane huɗu da ƙoƙon kan ɗan adam

Shugaban hukumar kwana-kwana, Dr Liman Ibrahim, ya yi alawadai da farmakin kuma ya lashi takobin tabbatar da an kama wadanda suka yi wannan aika-aika an hukunta su.

Kamar yadda shugaban hukumar ya ce:

“Jami’an zasu dakatar da aikin su ga duk gwamnatin jihar da ba za ta iya kulawa da rayukan jami’an hukumar da kayan aikin su ba.”

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel