Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna

Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna

  • Yar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta nuna jin daɗinta bisa kalaman soyayya da mijinta Ahmad Indimi ya yi a kanta
  • Zahra Buhari ta bayyana cewa ta yi sa'ar abokin rayuwa da ya kasance gwarzo a cikin maza
  • Zahra Muhammadu Buhari, da mijinta Ahmad Indimi, sun zama ma'aurata ne a shekarar 2016

Abuja - Ɗiyar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Zahra Buhari, ta yabawa abokin rayuwarta Ahmad Indimi, cikin soyayya da kauna, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Zahra ta yabawa mijin nata ne kasancewarsa abokin rayuwa nagari na tsawon shekarun da suka shafe tare da juna.

Zahra Buhari da Ahmad Indimi
Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna Hoto: Mrs_zmbi
Asali: Instagram

Ahmad Indimi, ya garzaya shafinsa na kafar sada zumunta Instagram, inda ya yi rubutu kan nasarar da ya samu wajen zaɓen abokiyar rayuwa, yace:

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

"Nasarar aure na bukatar faɗawa soyayya a lokuta da dama kuma kowane lokaci ina sake faɗawa soyayya da mutum ɗaya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya yi wanna rubutun na soyayya ga matarsa, Ahmad ya alakanta rubutunsa da shafin Zahra Buhari.

Zahra Buhari ta yaba wa mijinta

Da take martani kan wannan rubutu, Zahra Buhari tace:

"Ƙa rufe mun baki saboda tsantsar jin daɗi da farin ciki. Tabbas wannan wani ɓangare ne na rayuwar mu, babu matar da takai ni dace da samun miji nagari kamar ka na tsawon shekaru 5."

Zahra Muhammadu Buhari, da mijinta, Ahmad Indimi, sun yi aure ne a shekarar 2016, shekaru biyar kenan da suka shuɗe.

Yusuf Buhari ya angwance

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoto kan bikin ɗan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Yusuf, wanda ya auri ɗiyar sarkin Bichi, Zahra Bayero.

Kara karanta wannan

‘Yar Jafar Mahmud Adam ta haihu, an rada wa yaro sunan 'danuwanta da ya rasu a hadarin mota

Babu shakka garin Bichi dake jihar Kano ya cika dankam da jiga-jigai na fadin kasar nan har da kasashen ketare, wadanda suka dinga tururuwar zuwa shaida daurin auren.

Ministoci, gwamnoni, fitattun 'yan siyasa da masu fada a ji naa kasar nan sun shaida daurin auren, wanda aka daura kan sadaki N500,000.

A wani labarin kuma Mijin Kasar Italy Ya Harbe Matarsa Yar Najeriya Har Lahira a Gaban Abokan Aikinta, FG Ta Shiga Lamarin

Gwamnatin tarayya ta nemi a yi cikakken bincike kan musabbabin kashe matar aure yar Najeriya, Rita Amenze, a kasar Italiya.

Rahoto ya nuna cewa mijin ɗan kimanin shekara 61, ya aikata haka ne biyo bayan shigar da bukatar saki da matar ta yi gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262