Mijin Kasar Italy Ya Harbe Matarsa Yar Najeriya Har Lahira a Gaban Abokan Aikinta, FG Ta Shiga Lamarin

Mijin Kasar Italy Ya Harbe Matarsa Yar Najeriya Har Lahira a Gaban Abokan Aikinta, FG Ta Shiga Lamarin

  • Wani mutumi ɗan kasar Italiya, ya harbe matarsa yar Najeriya har lahira a kamfanin da take aiki
  • Rahoto ya nuna cewa mijin ɗan kimanin shekara 61, ya aikata haka ne biyo bayan shigar da bukatar saki da matar ta yi gaban kotu
  • Ofishin jakadancin Najeriya a Italiya ya sha alwashin karɓo wa matar da aka kashe hakkinta

Abuja - Gwamnatin tarayya ta nemi a yi cikakken bincike kan musabbabin kashe matar aure yar Najeriya, Rita Amenze, a kasar Italiya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A wani jawabi da shugaban hukumar kula da yan Najeriya na kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya bayyana kisan matar wanda mijinta ya yi da lamari ne mara ɗaɗi.

Kara karanta wannan

Ba tsaro a Najeriya, sai zubar da jini ake, inji Sule Lamido yayin ganawa da Obasanjo

Jakadan Najeriya a Italiya, Mfawa Omini Abam, shugaban NIDCOM, Dabiri-Erewa, da yan Najeriya dake zaune a kasar sun bukaci hukumomin tsaron Italiya su binciki lamarin kuma su tabbatar an yi adalci.

Amenze yar Najeriya a Italy
Mijin Kasar Italy Ya Harbe Matarsa Yar Najeriya Har Lahira a Gaban Abokan Aikinta, FG Ta Shiga Lamarin Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Meyasa mijin ya kashe matarsa?

Amenze yar kimanin shekara 31, ta shiga kasar Italiya ne a shekarar 2017 ta hanyar Libya, kuma ana zargin mijinta ɗan shekara 61, Pierangelo Pellizzar, da kashe ta har lahira bayan ta nemi kotu ta raba aurensu.

Rahoto ya nuna cewa, Pellizzar ya bindige ta sau huɗu a gaban abokan aikinta a wurin aje motocina kamfanin Mf Mushroom, inda take aiki, ranar Jumu'a da safe.

Amenze da mijinta Pellizzar ɗan asalin ƙasar Italiya, sun yi aure ne a shekarar 2018, shekara ɗaya bayan zuwan Amenze ƙasar.

Yan sanda sun cafke mutumin

Kara karanta wannan

Dan majalisar Adamawa ya bayyana makudan kudaden da kowanne dan majalisa ke samu don ayyukan mazabu

Shugaban ƙungiyar yan Najeriya dake zaune a ƙasar Italiya, (NUNAI), Mr Rowland Ndukuba, ya yi Allah wadai da kisan kuma ya godewa yan sanda da suka cafke wanda ya aikata kisan.

Bugu da ƙari, dailytrust ta rahoto jakadan Najeriya a Italiya ya tabbatar da cewa ofishinsa ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da anyi binciken da ya dace kan lamarin.

A wani labarin kuma Al'ummar Sokoto Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Aike Musu Wasikar Barazana

Yan bindigan da suka gudo daga jihar Zamfara , waɗanda suka kai hari kan kauyukan dake bakin boda a Sokoto makon da ya shuɗe, sun aike da wasikar cigaba da miyagun ayyukansu ga mutanen yankin.

Lamarin ya jefa mutanen yankunan cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar kan yaushe maharan zasu shigo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel