Labari Mai Daɗi: Jihar Kogi Za Ta Fara Samar da Man Fetur, Yahaya Bello

Labari Mai Daɗi: Jihar Kogi Za Ta Fara Samar da Man Fetur, Yahaya Bello

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce yanzu jihar Kogi za ta iya samar da man fetur
  • Gwamnan ya fadi hakan ne bayan kammala taro da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja
  • Ya kuma yi alkawarin amfani da kudaden da man zai samar da cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasa

FCT, Abuja - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana cewa yanzu jihar Kogi ta na samar da man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da manema labaran cikin gidan gwamnati suka yi da shi bayan ya kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Labari mai dadi: Jihar Kogi Za ta Fara Samar Da Man Fetur, Yahaya Bello
Labari mai dadi: Jihar Kogi Za ta Fara Samar Da Man Fetur, Yahaya Bello. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Gwamnan ya ce ya kai wa shugaban kasa ziyara ne don godiya bisa karamcin da ya yi masa da kuma yi wa mutanen sa sambarka, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga 3: NAF ta fara gwada sabbin jiragen Super Tucano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi alkawarin amfani da kudaden man wurin samar da ci gaba wurin bunkasa tattalin arzikin sauran bangarori don gudun sauran kura-kuran da kasa ta tafka a baya.

Ya bukaci shugaban kasa ya yi gaggawar kammala gyaran kamfanin Ajaokuta Steel kafin wa’adin mulkin sa ya kare.

A cewar sa:

“Na zo ne musamman don ganin mahaifina, shugaban kasa don yi masa godiya a maimakon daukacin jama’an jihar Kogi, Kogi ita ce jihar arewa ta farko da ta fara samar da man fetur.
“Mun zo don yi wa shugaban kasa godiya bisa karamcin da ya yi mana, kuma ina so in taya mutanen jihar Kogi murna da ‘yan Najeriya gaba daya. Muna rokon shugaban kasa ya taimaka ya kammala gina kamfanin Ajaokuta Steel, muna bukatar ya yi hakan kafin wa’adin sa ya kare.

Kara karanta wannan

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

“Sannan shugaban kasa ya yi farin ciki da hakan inda ya lashi takobin dawo da Ajaokuta da ranta kafin ya sauka daga mulki.
“Tunda yanzu muna samar da man fetur, ina so in tabbatar wa da jama’an jihar Kogi da ‘yan Najeriya cewa ba za mu sake maimaita kuskure da muka yi a baya ba inda Najeriya ta dogara da man fetur kadai a matsayin hanyar samar da kudin shiga.
"Duk abinda jihar Kogi za ta samar za a yi amfani da shi ne wurin bunkasa sauran bangarori, bangaren noma da dai sauran su don bunkasa tattalin arzikin kasa. Wannan hanyar ne za ta bubbugo da sauran bangarori. Ba za mu maimaita kuskuren da muka yi a baya ba.”

'Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun sace mutum 20 a Sokoto

A wani labari na daban, 'yan bindigan da ake zargin sun tsere ne daga daga yankunan Bakura - Talata Mafara na jihar Zamfara, a ranar Talata, sun kai hari ƙaramar hukumar Dange Shuni a Sokoto sun sace a ƙalla mutum 20, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sojojin Guinea suka kame shugaban kasa, suka kwace mulki

A halin yanzu dai rundunar sojojin Nigeria da wasu hukumomin tsaro suna aikin ragargazar ƴan bindiga a dazukan Zamfara.

Saboda aikin da sojojin ke yi an datse hanyoyin sadarwa na salula da kuma kasuwannin sayar da dabbobi da dakatar da sayar da fetur a jarka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel