NAPTIP: Rashin jituwa da Minista Sadiya Faruk ya sa aka fatattaki tsohon sanata

NAPTIP: Rashin jituwa da Minista Sadiya Faruk ya sa aka fatattaki tsohon sanata

  • Bincike ya nuna cewa, minista Sadiya Umar Farouk ce ta bukaci a tube Sanata Basheer Mohammed daga shugabancin NAPTIP
  • An sanarwar da sallamar tsohon sanatan daga hukumar, ministan ta ce akwai bukatar wanda zai jajirce domin cigaban hukumar
  • Da kan ta ministan ta mika sunan Fatima Waziri-Azi a matsayin wacce za ta maye gurbin Sanatan ganin irin gogewarta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Sanata Basheer Mohammed, darakta janar na hukumar yaki da safarar jama'a (NAPTIP).

Daily Trust ta ruwaito cewa, an sallami Mohammed kasa da watanni hudu da ya karbi ragamar hukumar.

A wata takarda ta ranar Laraba, babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce shugaban kasan ya amince da nadin Fatima Waziri-Azi a madadin Mohammed.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

NAPTIP: Rashin jituwa da Minista Sadiya Faruk ya sa aka fatattaki tsohon sanata
NAPTIP: Rashin jituwa da Minista Sadiya Faruk ya sa aka fatattaki tsohon sanata. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shehu ya ce an yi nadin ne sakamakon bukatar ministan walwala da jin kan 'yan kasa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce ministan ta nuna bukatar gaggawa ta ma'aikatar wurin kara karfin NAPTIP domin a cimma bukatar da ake so.

Ya bayyana cewa, Hajiya Sadiya ta ce ta mika Fatima Waziri-Azi ne saboda gogewarta da kuma bibiyar ayyukanta da aka yi wanda aka tabbatar zai ciyar da hukumar gaba.

Karfin ikon ministan a ma'aikatar ne yasa aka sallami sanatan da ya taba wakiltar mazabar Kano ta tsakiya daga 2011 zuwa 2015 a majalisar dattawa, Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa, babu jituwa tsakanin shi da ministan, lamarin da yasa aka sauke shi.

Kafin nadin shi a matsayin shugaban NAPTIP a watan Mayu na wannan shekarar, shi ne kwamishinan tarayya na hukumar kula da 'yan gudun hijira, masu shigowa kasar nan da kuma wadanda suka rasa muhallinsu.

Kara karanta wannan

Hisbah Ta Kama Motoci Biyu Maƙare Da Katon Ɗin Giya 5,760 a Kano

A watan Augustan 2019, ya maye gurbin Sadiya a hukumar masu neman mafaka bayan an nada ta a matsayin minista.

'Yan fashin daji sun sheke dan sanda 1, sun iza keyar mutum 23 a yankunan Kaduna

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun yi ajalin wani sifetan ‘yan sanda sannan sun yi garkuwa da mutane 23 sakamakon wani hari da suka kai Unguwan Maje da Unguwan Laka da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

TheCable ta fahimci yadda ‘yan bindigan suka kai farmakin da safiyar ranar Laraba.

An samu bayanai a kan yadda suka yi ta harbe-harbe ‘yan kauyen suna gudun neman tsira, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng