Mahaifiyar Sunday Igboho da Yarbawa sun gargadi Sheikh Gumi cewa ya nisanci yankinsu

Mahaifiyar Sunday Igboho da Yarbawa sun gargadi Sheikh Gumi cewa ya nisanci yankinsu

  • Shugabanni a yankin Yarbawa sun gargadi Sheikh Gumi kan zuwa yankin su Sunday Igboho
  • Wannan na zuwa ne bayan da malamin ya ziyarci garinsu Sunday Igboho a makon da ya gabata
  • Ciki har da mahaifiyar Igboho, an yi addu'o'in wanke sharrin da malamin (Gumi) ya zo dashi yankin

Igboho, jihar Oyo - Magoya bayan dan awaren yarbawa Sunday Igboho, mahaifiyarsa da danginsa sun gargadi malamin addinin musulunci dan Arewa, Sheikh Ahmad Gumi da ya nesanta kansa daga kasar Yarbawa.

Sun bayyana ziyarar da Gumi ya kai garinsu Igboho a matsayin abin ''tuhuma'' kuma ''rashin hankali '.

Igboho, dan shekaru 48 a halin yanzu yana garkame a hannun jami'an jamhuriyar Benin bisa wasu laifuka ciki har da kutse cikin kasa ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

Mahaifiyar Sunday Igboho da Yarbawa sun gargadi Sheikh Gumi cewa ya nisanci yankinsu
Dattawa a yankin Yarbawa da mahaifiyar Sunday Igboho sun nemi Gumi ya nisanci yankinsu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Rahotanni sun bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga Sheikh Gumi tare da tsohon babban jami'in hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Usman Yusuf a kusa allon makarantae 'Muslim Grammar School, Modeke, Igboho' a ranar 7 ga watan Satumba.

Da yake magana yayin ziyarar, malamin ya ce da abin da ya gani, babu bukatar wata kungiya ta nemi ballewa daga Najeriya.

A wani bidiyon bidiyo da The Nation tace ta samu a karshen mako, Sheikh Abdul Raheem Aduanigba, Babban Limamin Yarbawa a Ilorin, ya jagoranci wasu shugabanni zuwa garin Igboho tare da mahaifiyar Igboho.

Sun ziyarci wurin da Gumi ya yi wancan bidiyon yayin ziyararsa a garin sannan kuma sun yi addu’o’i don rushe munanan dalilai da suka kawo Gumi garin.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Ziyarar Da Sheikh Gumi Ya Kai Garin Igboho 'Neman Rigima' Ne, In Ji Basarekan Yarbawa, Gani Adams

“Ba mu san lokacin da Gumi ya zo nan ba, Igboho bai damu da dukiyarsa ba, ya kan kashe kudi da yawa. Ya kan kula da kowa har da Musulmai.
“Muna addu’ar nasara don a saki Igboho. Allah zai daow da Igboho gida lafiya ya sadu da mahaifiyarsa. Allah ya kiyaye Igboho ya ba shi tsawon rai. Babu zaman lafiya a Najeriya. Dole ne mu yi taka tsan-tsan a Najeriya.”

Daya daga cikin abokan Igboho, Alhaji Yusuf Saheed wanda aka fi sani da Ajikobi 1 ya ce:

“Shi (Gumi) kawai ya zo nan cikin rashin sani ne, kuma ya yi amfani da kusan mintuna 3. Igboho mutum ne mai karfin ikon gaske, duk da tsoratarwar da gwamnati ke yi masa, har yanzu yana nan daram.”

Sheikh Gumi: Da yawan shanun da ake sacewa a Arewa 'yan Kudu ake sayarwa

Malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya bayyana cewa mafi yawan shanun da aka sace a jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa maso yammacin kasar ana jigilar su zuwa kudancin kasar ne - kudu maso gabas, kudu maso kudu da kudu maso yamma a matsayin abinci.

Kara karanta wannan

Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar

Ya yi wannan fallasa mai ban al'ajabi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook ranar Litinin, 6 ga Satumba.

A cewarsa, wannan satar ta taimaka wajen kara ta'azzarar matsalar 'yan bindiga da ake fuskanta a kasar a yau ba kadan ba.

A cewar Gumi:

"Daga cikin halin da ake ciki, a shekarar 2009 satar shanu ya zama ruwan dare. Yawancin shanun da aka sace sun nufi kudu dasu a cikin tirela inda ake siyarwa ana yanka su.
"Wannan babban jigila na satar shanu ya rage yawan samar dasu. Mafi yawan satar da farko ya shafi makiyaya na karkara kuma ya zama mafi yawa a yankin Arewa maso yamma."

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

A wani labarin, Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Bidiyo ya bayyana yayin da Sheikh Gumi ya ziyarci mahaifar Sunday Igboho

A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.

A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.